Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi harbe-harbe a kasar Amurka
2019-07-29 20:47:11        cri
An yi harbe-harbe a birnin Gilroy dake jihar California ta kasar Amurka a jiya, 'yan sandan wurin sun tabbatar da cewa, mutane 4 sun mutu a sakamakon lamarin, kana mutane 15 sun ji rauni.

Shugaban hukumar 'yan sanda ta birnin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana da dare cewa, lamarin ya faru ne a bikin tafarnuwa na shekara-shekara, inda mutane fiye da dubu daya suka taru domin taya juna murnar bikin. Har yanzu, ba a san dalilin da ya sa maharin ya yi ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China