Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Nijeriya: Takaddamar ciniki da Amurka ta tada ta kawo illa ga kanta da kuma sauran kasashe
2019-06-12 14:07:49        cri

A jiya ne, direktan cibiyar nazarin harkokin Sin dake Nijeriya Charles Onunaiju ya gabatar da bayani mai taken "gaskiyar sakamakon da aka samu domin takaddamar ciniki a tsakanin Sin da Amurka" a jaridar Peoples Daily da sauran kafofin watsa labaru, inda ya zargi kasar Amurka ta tada takaddamar ciniki a tsakaninta da kasar Sin ba tare da tushe ba.

Cikin bayanansa ya ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya tada takaddamar ciniki a duniya, musamman kara kudin harajin kwastam ga kasar Sin, da dalilinsa na zama matsayin fuskantar ciniki maras adalci. Sin da Amurka suna da fifiko daban a ciniki, wanda zai iya sa kaimi ga samun bunkasuwa a tsakaninsu, har ma da samun ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. Shugaba Trump ya tada takaddamar ciniki ga Sin, da kungiyar EU, da Canada, da Japan, har ma da Mexico da sauran kasashen duniya, wadda ta kawo illa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya ta hanyar siyasa, ba tare da yin la'akari da hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa ba.

Bayanin ya yi tsammani cewa, rikicin harajin kwastam a tsakanin manyan kasashen tattalin arzikin duniya zai kawo illa ga kasuwar duniya, da kawo rashin tabbas ga kasashen saurin ci gaban tattalin arziki kamar Nijeriya. Takaddamar ciniki da Amurka ta tada ta kawo illa ga kanta da kuma sauran kasashen duniya baki daya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China