Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An Bayyana Kudin aikin Hajjin Bana na Yankin Abuja
2019-05-20 14:07:02        cri
Bisa labarin da muka samu daga shafin jaridar Leadershipayau, Hukumar Alhazai ta babban birnin Tarayyar Nijeriya wato Abuja, ta amince da biyan Naira miliyan 1.5 a matsayin kudin aikin hajjin bana, ga maniyyatan da suke son tashi daga Abujan.

Kakakin hukumar, Muhammad Lawal, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce, an kayyadewa duk maniyyatan da za su tashi daga Abuja, samun canjin kudi wajen Dala 800, kamar yadda hukumar aikin hajjin ta kasar NAHCON, ta kayyade.

Muhammad Lawal, ya bayyana cewa, karin da aka samu na kudin aikin hajjin bisa na bara, ya biyo bayan karin da aka samu na ayyukan da ake yi wa alhazan a can kasa mai tsarki, da kuma karin da aka samu a kan canjin Naira zuwa dala, yana mai jaddada kudurin hukumar na yin dukkan mai yuwuwa, wajen ganin ta yi wa alhazan bana abun da ya kamata.

Ya kara da cewa, hukumar na kira ga dukkanin maniyyatan da suka fara ajiya a asusun aikin hajjin da su hanzarta cika sauran kudin kafin ranar 31 ga watan Mayu, domin hukumar ta sami cimma wa'adin da hukumar NAHCON ta kasa ta ba ta.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China