Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wu Haitao: Sin na goyon bayan kara inganta tsarin gudanar da ayyukan kwamitin tsaron MDD
2019-06-07 16:42:56        cri
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ce Sin na matukar goyon bayan kara inganta tsarin gudanar da ayyukan kwamitin tsaron MDD, ta yadda hakan zai ba da damar kyautata sauke nauyin dake wuyan kwamitin, bisa tanajin dokokin MDD.

Jami'in ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin taron muhawarar kwamitin na tsaro, yana mai cewa, kwamitin na da wani muhimmin nauyi na tabbatar da daidaito a sha'anin zaman lafiya, da tsaron kasa da kasa, kuma tabbatar da ingancin aikin sa, nauyi ne dake wuyan daukacin kasashe mambobin sa.

Domin cimma wannan buri, wakilin na Sin ya ce, kamata ya yi kwamitin ya mayar da hankali ga muhimman ayyukan sa bisa dokokin da suka kafa shi, musamman ma batun dakile al'amuran dake barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, maimakon mayar da hankali kan tsoma baki cikin harkokin daidaikun kasashe, wadanda ba sa wata barazana ga tsaro, da zaman lafiyar duniya.

Daga nan sai Wu Haitao, ya bayyana aniyar kasar Sin, ta share hanya ga sabbin zababbun mambobi marasa kujerun dindindin a kwamitin na tsaro, ta yadda za su samu zarafin gudanar da ayyukan su yadda ya kamata. Ya ce kamata ya yi a baiwa sabbin mambobin dama ta bai daya, ta yadda za su samu ikon ba da gudunmawa, a fannin warware muhimman batutuwa dake gaban kwamitin.(Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China