Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UN-Habitat: ana mai da hankali kan raya birane masu dorewa
2019-05-30 11:21:23        cri

A Jiya Laraba ne aka bude taron manyan jami'ai na babban taron UN-Habitat karo na farko a birnin Nairobi hedkwatar kasar Kenya, inda shugabannin kasashen Kenya, da Sudan ta Kudu, da na sauran kasashe suka yi kira ga kasashen duniya, da su kara goyon bayan hukumar UN-Habitat, a kokarin tinkarar kalubalolin da ake fuskanta wajen raya birane, kamar gidajen kwana, da samun aikin yi da sauyin yanayi.

A yayin taron, Uhuru Kenyatta, shugaban kasar Kenya ya ce, yayin da ake raya birane a duk fadin duniya, kasashen duniya, musamman ma kasashe masu tasowa, suna fuskantar babban kalubale, kamar gidajen kwana.

Gwamnatocin suna bukatar sabunta hanyoyinsu, da karfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, wajen shiga ayyukan warware matsalar gidajen kwana, tare da samar musu kyakkyawan yanayin kasuwanci da zuba jari.

A yayin taron manema labaru da aka yi a jiya, madam Maimunah Mohd Sharif, darektar zartaswa ta hukumar UN-Habitat ta ce, gwamnatocin kasashe 38, da hukumomi 32, sun yi alkawarin bai wa hukumarta tallafin kudi fiye da dalar Amurka miliyan 152, wajen mara wa hukumar baya kan tabbatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD, da kuma manufofin da suka shafi raya birane. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China