Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNHCR ta damu game da tashe-tashen hankulan Najeriya dake raba al'ummu da muhallan su
2019-05-29 09:15:26        cri
Kakakin hukumar MDD mai lura da harkokin 'yan gudun hijira ko UNHCR a takaice Babar Baloch, ya nuna damuwa game da karuwar tashe-tashen hankula a arewa maso yammacin Najeriya, lamarin dake raba dubban al'ummu da muhallan su.

Mr. Baloch ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin wata ganawa da manema labarai, yana mai cewa ya zuwa watan Afrilun bana, yawan 'yan Najeriya dake neman mafaka a sassan jamhuriyar Nijar ya kai mutum 20,000.

Ya ce hukumarsa na aiki tare da mahukuntan jamhuriyar Nijar, wajen samar da ababen bukatun yau da kullum, ga dubban al'ummun da suka samu matsuguni, da ma wadanda ake yiwa rajista a halin yanzu. Jami'in ya ce kawo yanzu, an riga an yiwa mutane 18,000 rajista a wuraren da aka tsugunar da su.

Ya ce cikin kungiyoyin da suke haddasa tashe-tashen hankula a yanzu hadda wata mai alaka da kungiyar IS, maimakon Boko Haram wadda a baya ta yi mummunan tasiri. Kaza lika ana fuskantar zaman doya da manja tsakanin manoma da makiyaya a wasu yankuna, da matsalar kungiyoyin masu dauke da makamai, da masu garkuwa da jama'a don neman kudin fansa a jihohin Sokoto da Zamfara. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China