Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi bikin ranar keke ta duniya
2019-06-04 11:51:01        cri

MDD ta gudanar da bikin ranar Keke ta duniya a jiya Litini, domin yabawa yanayinsa na musammam da dadewarsa da kuma alfanunsa mabanbanta.

Da take jawabi, shugabar babban zauren majalisar, Maria Fernanda Espinosa Garces, ta ce kekuna za su iya bada gagarumar gudunmuwa, daga rage hayakin da ababen hawa ke fitarwa da mace-macen da ake yi sanadiyyar haddura, zuwa rage kiba da cututtukan da ba sa yaduwa da inganta sadarwar sufuri a yankunan karkara da kuma karfafa gwiwar mata da 'yan mata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China