Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta tsawaita takunkumin da aka sanyawa Sudan ta Kudu zuwa karin shekarar guda
2019-05-31 11:04:12        cri
A jiya Alhamis kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa'adin takunkumin haramta sayar da makamai ga Sudan ta Kudu na tsawon shekara guda har zuwa ranar 31 ga watan Mayun 2020.

Kudurin dokar mai lamba 2471 an amince da shi ne bayan mambobin kasashe 10 suka kada kuri'ar amincewa yayin da 5 suka janye jiki daga jefa kuri'a, daga cikinsu akwai kasashe uku daga Afrika sai kuma kasashen Sin da Rasha.

Matakin tsawaita takunkumin na shekara guda, ya shafi daskarar da kadarori, gami da haramta tafi ketare ga wasu 'yan kasar ta Sudan ta kudu su takwas bisa irin rawar da suke takawa wajen ruruta wutar tashin hankali a kasar.

Zartaswar kudurin na bukatar samun kuri'u 9 ne daga cikin mambobin kwamitin MDD 15, sa'an nan babu kasa guda daga cikin wakilan kasashe masu wakilcin dindindin a MDD da suka ki amincewa da kudirin, wadanda suka hada da kasashen Amurka, Rasha, Sin, Faransa, da Birtaniya.

Jerry Matjila, wakilin kasar Afrika ta Kudu a MDD, ya ce, bisa la'akari da yanayin siyasa da ake ciki a Sudan ta Kudu, sanya takunkumin ba zai taimaka ba a wannan hali da ake ciki.

Ya bukaci kwamitin sulhun MDD da ya goyi bayan yunkurin da kungiyar raya kasashen gabashin Afrika (IGAD), da kungiyar tarayyar Afrika (AU) suke yi a Sudan ta Kudun. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China