Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu sama da ragin Yuan biliyan 500 a watanni hudu na farkon bana a sabbin harajin da kasar Sin kaddamar
2019-05-31 10:51:18        cri

Wasu alkaluma da hukumar kula da harkokin haraji ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, manufofin rage kudaden harajin da kasar ta bullo da su, sun taimakawa wajen ragewa 'yan kasuwa da daidaikon mutane kudaden da suka kai Yuan biliyan 524.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 76 a watanni hudu na farkon wannan shekara.

Hukumar ta ce, rage harajin kayayyakin, wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Afrilu, ya taimaka wajen rage kudaden harajin da suka kai Yuan biliyan 111.3.

Da yake karin haske kan wannan ci gaba da aka samu, Farfesa Lyu Bingyang na Jami'ar Renmin dake nan kasar Sin, ya bayyana cewa, bangaren samar da kayayyakin kasar, shi ne ya fi cin gajiyar rangwamen harajin na VAT. Sauran matakan da suka hada da yiwa tsarin harajin na VAT gyaran fuska, sun kai ga bangaren samar da kayayyaki fara amfana da sabon ragin harajin na Yuan biliyan 47.6 a watan Afrilu, wanda ya kasance na farko daga cikin dukkan sassa.

Lyu ya ce, ragewa bangaren samar da kayayyakin kasar haraji, ba kawai zai taimaka wajen rage kudaden dawainiya gami da inganta harkokin kasuwancin sashen kadai ba, har ma zai amfani sauran sassa ta hanyar bullo da hanyoyin samar da kayayyaki.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China