Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Najeriya ta kara yawan jarin kamfanonin Inshora
2019-05-22 10:05:16        cri
Gwamnatin Najeriya ta sanar da kara yawan jarin bangarorin dake kula da harkokin inshorar kasar. Shugaban hukumar kula da ishora ta Najeriya Salami Rassaq ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe.

Ya ce, an kara jari mafi kankanta na kamfanonin inshora zuwa Naira biliyan 8 daga Naira biliyan biyu, kwatankwacin dalar Amirka miliyan biyar, yayin da aka kara jarin inshorar gama-gari, daga Naira biliyan uku zuwa Naira biliyan 10.

Jami'in ya ce, an kuma kara jarin kamfanin dake ba da hidimar ishora daga Naira biliyan biyar zuwa Naira biliyan 18, yayin da aka kara jarin ishoran da kamfanoni ke saya daga Naira biliyan 10 zuwa Naira biliyan 20.

Rasaaq ya ce, karin jari mafi kankanta da aka sanya, zai fara aiki ne tun daga ranar 20 ga watan Mayu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China