Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta kaddamar da gangamin kawo karshen yin bahaya a wajen ban dakuna nan da shekarar 2025
2019-05-10 09:31:01        cri
Gwamnatin Najeriya ta amince da kafa wani shirin gangamin wayar da kai na kasa a kokarin da take na kawo karshen yin bahaya a wajen ban dakuna nan da shekarar 2025.

Ministan albarkatun ruwa Suleiman Adamu ya bayyanawa 'yan jaridu cewa gwamnatin Najeriyar ta amince da samar da kudade daga cikin kasafin kudin kasar na shekara da kuma kudaden da kungiyoyin raya ci gaba ke bayarwa domin gangamin wayar da kai na kasa mai taken "Tsabtace Najeriya, ta hanyar amfani da ban dakuna."

Kananan hukumomi 10 daga cikin adadin kananan hukumomin Najeriya 774 ne ba su yin bahaya a waje. Kuma wadannan alkaluma sun nuna cewa al'ummonin yankuna 21,000 a kasar ta yammacin Afrika ne kadai suke kaucewa yin bahaya ba'a cikin ban dakuna ba, in ji Adamu.

Jami'in ya nanata cewa, gangamin ya zama tilas kasancewar matsalar kazanta a Najeriya tana ci gaba da karuwa kuma al'amarin ya yi muni, yayin da kusan mutane miliyan 47 ne a kasar har yanzu ke ci gaba da yin bahaya ba a cikin ban dakuna ba.

Najeriya ce kasa ta biyu bayan kasar Indiya wadanda ke sahun gaba a cikin kasashen duniya dake yin bahaya ba a cikin ban dakuna ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da majalisar ministocinsa sun amince za su zama jakadu a jahun farko na gangamin wayar da kai don kawo karshen dabi'ar yin bahaya ba a cikin ban dakuna ba, ta hanyar samar da ingantaccen tsarin shugabanci da kyawawan manufofi don samun nasarar aiwatar da shirin yaki da muguwar dabi'ar yin bahaya a wajen bandakuna. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China