Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Maaunin GDP na Nijeriya ya karu da kaso 2.01 a cikin rubuin farko na bana
2019-05-21 09:37:18        cri

Hukumar kididdiga ta Nijeriya, ta ce ma'aunin tattalin arzikin kasar wato GDP, ya karu da kaso 2.01 a cikin rubu'in farko na bana.

Yanayin yawan karin da aka samu na baya-bayan nan ya dara kaso 1.89 da aka samu a rubu'in farko na 2018 da kaso 0.12.

Hukumar ta ce akwai yuwuwar ci gaban tattalin arzikin da aka samu na da alaka da babban zaben kasar da aka gudanar a rubu'in na farko.

Ta kara da cewa, karuwar GDPn cikin rubu'in na farko ya dara wanda aka samu a makamancin lokacin a shekarar 2018 da kaso 2.54.

Tattalin arzikin Nijeriya dai, ya dagora ne kan man fetur da wasu bangarori da ba na mai ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China