Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya tana neman tallafin MDD wajen farfado da yankunan da rikici ya daidaita a arewa maso gabashin kasar
2019-05-08 10:32:16        cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da bukatar neman agaji ga MDD da al'ummar kasashen duniya domin taimakawa kasar wajen farfado da yankunan da rikicin mayakan Boko Haram ya tarwatsa a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Da yake jawabi a lokacin ganawa da shugabar taron MDD karo na 73 na babban zauren MDDr (UNGA), Maria Fernanda Espinosa a Abuja, shugaban na Najeriya ya ce, halin yanayin rayuwar mutanen dake zaune a sansanonin 'yan gudun hijiri ke ciki abin tausayi ne.

"Muna da miliyoyin kananan yara wadanda ba su ma san iyayensu ba, ballantana daga inda suka fito," in ji shugaban.

Shugaba Buhari ya fadawa bakuwar tasa cewa, mayakan Boko Haram sun lalata muhimman kayayyakin more rayuwa, musamman a shiyyar arewa maso gabashin kasar, barnar ta wuce misali, sun lalata gadoji, da makarantu, asibitoci, coci-coci, masallatai, da sauran muhimman gine-gine.

"Dukkan wadannan kayayyaki ana bukatar a farfado da su, kuma duk wani nau'in taimako da aka samu daga kasa da kasa ana maraba da shi," in ji shugaban Najeriyar.

Shugabar ta UNGA ta yabawa Najeriya kasancewarta muhimmiyar jigo ga ayyukan MDD, ta kara da cewa, ana girmama Najeriyar a duk fadin kasashen duniya.

"Najeriya jigo ce wajen bada gudunmmawa ga ayyukan tabbatar da zaman lafiyar duniya, kuma muhimmin bangare ne wajen tabbatar da gina tsarin 'yancin dan adam," in ji Espinosa.

Ta yi alkawarin gabatar da yin kira don janyo hankalin kasashen duniya domin su bada fifiko kan batun shawo kan matslolin da tafkin Chadi ke fuskanta da sauran batutuwan da shugaban Najeriyar ya gabatar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China