Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
EFCC za ta binciki shugaban majalissar dattawa
2019-05-15 10:07:12        cri
Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ko EFCC a takaice, ta ce ta fara bincikar shugaban majalissar dattijan kasar Bukola Saraki.

Shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Magu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Talata, a Abuja fadar mulkin kasar, yana mai cewa binciken ba shi da wata boyayyiyar manufa. Magu ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin alakakai ga Najeriya, kuma wani tushe na dukkanin wata matsala da kasar ke fuskanta.

EFCC ta ce ta fara gudanar da sabon bincike a kan yadda sanata Saraki ya gudanar da shugabancin majalissar dattawan kasar, da kuma irin kudaden da ya karba a matsayin sa na gwamnan jihar Kwara, tsakanin shekarun 2003 zuwa 2011.

To sai dai a nasa bangare, Sanata Saraki ya jaddada kin amincewar sa da manufar binciken, yana mai bayyana shi a matsayin wani mataki na bita da kulli. Ya ce matakin na EFCC ya tabbatar da zargin da suka dade suna yi cewa, ayyukan hukumar na cike da burin cimma bukatun kashin kai ko ramuwar gayya, wanda hakan ya sabawa dokokin Najeriya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China