Masu karatu, ko kuna son rage kiba, amma ba ku son rage cin abinci, balle ma motsa jiki da yawa? Yau ina da wani albishir. Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya gano cewa, za a iya rage kiba ba ta hanyoyin rage cin abinci da motsa jiki ba. Amma akwai sharadi na farko, wato a ci abinci cikin awoyi 10 a ko wace rana. Bayan an ci abinci na karshe na ko wace rana, to, kada a sake cin kome cikin awoyi 14 ban da ruwa. Ta haka za a iya rage kiba tare da kyautata Metabolic Syndrome.
Masu nazari daga cibiyar nazarin halittu na Salk na Amurka da reshen jami'ar California da ke San Diego ta Amurka sun gudanar da nazarinsu kan mutane 19 masu fama da Metabolic Syndrome. To, mene ma'anar Metabolic Syndrome ko kuma MS a takaice? Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, Metabolic Syndrome ko kuma MS a takaice, wani yanayi ne dake shafar kiba, sukari da furotin, tare da haifar da alamomin samun kiba a ciki, yawan sukarin cikin jini, hawan jiki da dai sauransu. Likita kan ba da shawarar rage cin abinci, kara motsa jiki da shan magani domin shawo kan ciwon.
A cikin nazarin, wadannan mutane 19 ba su rage cin abinci ko kara motsa jiki ba. Sai dai, su kan ci abinci cikin awoyi 10 a ko wace rana yayin da suke ci gaba da shan magani.
Sakamakon nazarin ya nuna mana cewa, bayan watanni 3 da gudanar da nazarin kansu, wadannan mutane 19 masu fama da ciwon MS sun kyautata yin barci, nauyin jikinsu, kibar dake tattara a cikinsu, kunkuminsu dukkansu sun rage da kashi 3 zuwa 4 cikin kashi 100, kana kuma hawan jininsu da kuma yawan sinadarin Cholesterol da ke jikinsu su ma sun ragu, haka lamarin yake a fannonin yawan sukari da ke jininsu da kuma sinadarin Insulin. Har ila yau suna cikin koshin lafiya a duk tsawon lokacin gudanarwar nazarin.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, cin abinci ta hanyar da ba ta dace ba yana illanta yadda mutane suke rayuwa a rana da kuma yin barci a dare, lamarin da ya kara barazanar samun matsalar sarrafa sinadaran jiki. Cin abinci cikin awoyi 10 a ko wace rana ya bai wa jikin dan Adam lokacin hutu da samun farfadowa na awoyi 14 a dare. A kwana a tashi, ana kyautata yadda ake rayuwa a rana da yin barci a dare, ta haka jikin dan Adam ya kan kiyasta lokacin cin abinci a ko wace rana, lamarin da ya kyautata yanayin sarrafa sinadaran jiki.
Masu nazarin Amurka sun nuna cewa, sun yi farin ciki da ganin kayyade tsawon lokacin cin abinci da kuma shan magani yadda ya kamata sun taimaka wa masu fama da MS yaki da ciwon. Kuma kayyade tsawon lokacin cin abinci ya fi rage cin abinci sauki. (Tasallah Yuan)