Yanzu haka jiragen kasa suna kaiwa da kawowa a tsakanin kasashen Sin da Turai, yayin da jiragen ruwa masu daukar kaya suke tafiya kan tekun kudancin kasar Sin da tekun Indiya, wadanda cike suke da manyan akwatuna. A duk inda kuke kasancewa, ko a tashar jirgin ruwa, ko a tashar jirgin kasa, ko a wurin aiki, ko a hamada, don Allah ku yi amfani da wayar salularku ko na'urar kyamara domin daukar hoto kan abubuwan da kuka gani. Hotunan da kuka dauka za su nuna yadda mu 'yan Adam muke sada zumunta da mu'amala da juna a karni na 21.
Muna maraba da hotunanku. Za mu kalli "ziri daya da hanya daya" cikin hotunanku tare da abokanmu.
I. Lokacin Tattara Hotuna
Tsakanin ranar 28 ga watan Fabrairu da ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2019.
II. Jigon Hotuna
Shawarar "Ziri daya da hanya daya" A Idonka/ki
III. Abubuwa Masu Alaka
1. Dole ne a gabatar da hotuna irin na digital da aka yi amfani da na'urar kyamara ko wayar salula aka dauka.
2. Za a iya samar da hoto daya kawai ko wasu hotuna masu launuka ko irin na baki da fari. Idan aka samar da hotuna, dole ne yawansu ya kai 3 ko fiye, amma bai kamata ya wuce guda 10 ba. Ana karbar hotuna ne da aka adana su da samfurin JPEG.
3. ko a ko wace kasa kake, za ka iya turo mana hotunan. Don Allah ka rubuta sunan mai daukar hoto, asalin kasarsa, hanyar tuntubarsa, wurin daukar hoton, taken hoton, da ma takaitaccen bayani kan hoton wanda ba zai wuce kalmomi 150 ba.
4. Ban da hoton, za ka iya kara rubuto mana labari kan hoton.
IV. Hanyar turo mana hoto
Za ka iya turo mana ta adireshin E-mail: withyou2019@qq.com.
V. Hanyar da za a bi wajen zabar mafiya kyau
Domin gudanar da wannan aiki cikin adalci yadda ya kamata, za mu hada hanyoyi biyu tare wajen zabar mafiya kyau, wato za mu gayyaci kwararrun da abin ya shafa su yi zabi, sa'an na za a jefa kuri'a kan hotunan a kan shafin Intanet.
VI. Lambobin yabo da aka kafa:
1. Wadanda suka samu manyan lambobin yabo guda 10 za su samu takardun lambobin yabo, tare kuma da halartar bikin karbar lambobin yabo da za a shirya a kasar Sin, da halartar ayyukan daukar hotuna da za a gudanar a kasar Sin.
2. Wadanda suka samu lambobin yabo da suka yi fice guda 100, za su samu takardun lambobin yabo da kyaututtuka (Misali: kayayyakin al'adu na cibiyar ajiye kayayyakin tarihin kasar Sin ta fadar sarakuna ta kasar, adikon siliki, na'urar karanta littattafai ta zamani da dai sauransu).
3. Wadanda suka samu lambar yabo ta labaru game da fitattun hotuna, za su samu kyaututtuka masu kyau(Misali: kayayyakin al'adu na cibiyar ajiye kayayyakin tarihin kasar Sin ta fadar sarakuna ta kasar).
VII. Ka'idojin gasar:
1. Ba za a mayar da hotunan da aka turo mana ba, bayan 'yan takara sun gabatar da hotunansu, to mai karbar bakuncin gasar zai su samu ikon amfani da su ba tare da biyan kudi ba, ko neman izni kafin baiwa sauran bangarorin dake kula da gasar ba. Ban da wannan kuma mai karbar bakuncin gasar na da ikon amfani da hotunan wajen bikin baje koli, furofaganda, madaba'a da dai sauransu.
2. Ana iya gyara hotuna kadan ta hanyar mahajar gyara hotuna amma ba za a iya gyara ainihin abun da aka dauka a cikin hotunan ba, kana ba za a iya karawa ko cire wani abu ko canja ainihin abun dake cikin hotun ba.
3. Idan aka gano wanda ya saci hotunan da sauran mutane suka dauka, za a soke masa iznin shiga gasar.
4. Za a shigar da hotunan da suka samu lambar yabo a gasar a cikin littafin hotuna na "Shawarar 'Ziri daya da hanya daya' A Idonka/ki", tare da gabatar da su a kan shafin Intanat na harsuna daban daban na CRIonline.
5. Babu bukatar biyan kudi ko kadan don shiga gasar.