Tare da fatan daukacin ma'aikatan sashen Hausa na CRI suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Ina farin cikin shaida muku cewa, na saurari wani Sharhi na CRI Hausa ta kafar yanar gizo dangane da bikin cika shekaru 40 da kaddamar da shirin yin kwaskwarima ga tattalin arzikin kasar Sin tare da bude kofa ga kasashen waje. Kamar yadda Hausawa kan ce, waiwaye adon tafiya. Hakika, shirin wannan shiri wanda marigayi shugaba Deng Xiaoping ya kaddamar a shekarar 1978 ya zama wani muhimmin bangare na tarihin kasar Sin na kimanin shekaru dubu biyar.
Ba shakka, wannan shiri da kasar Sin ta kaddamar shekaru 40 da suka gabata za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu. Domin ya haifar da gagarumin sauyi ta fannoni da dama, kama daga sha'anin tattalin arziki, cinikayya, bunkasar masana'antu da kere-kere, habakar birane, bunkasar harkokin sufuri da kuma uwa-uba babbar nasarar tsamo daruruwan miliyoyin Sinawa daga kangin talauci.
Hakika, shugabannin kasar Sin sun cancanci jinjina da yabo mai yawa tun daga kan wadanda suka kirkiro da wannan shiri zuwa sauran shugabanni da suka tsaya tsayin daka kuma suka jajirce har wannan gagarumar nasara ta tabbata. Domin ba Sinawa kadai ke mamakin nasarar ba, har ma da sauran al'ummar duniya na ta'ajibin irin gagarumar nasarar da kasar Sin ta cimma cikin shekaru arba'in, inda ta tashi daga kasa wacce al'ummarta ke fama da fadi tashin rayuwa zuwa kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya.
Wadannan nasarori da kasar Sin ta samu sun kara daga darajarta a duniya kuma tasirinta ya karu wajen sha'anin kasa da kasa, musamman irin rawar da kasar Sin ke takawa a fannin bunkasar tattalin arzikin duniya kamar yadda alkaluma suka nuna cewa ya kai kashi 30 cikin 100 a shekarar da ta gabata. Wannan babbar shaida ce da ke nuna cewa, ban da Sinawa, al'ummar duniya ma baki daya suna cikin gajiyar bunkasar tattalin arzikin kasar Sin. Domin kamfanonin kasar Sin suna samar da kayayyakin amfanin yau da kullum cikin farashi mai rangwame, lamarin dake kawo saukin gudanar da rayuwa ga kasashe masu tasowa musamman na nahiyar Afirka.
Yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke kara habaka a cikin shekaru na 2000, kasar Sin ta rungumi kasashe masu tasowa musamman na Afirka wadanda suka dade suna dandana kudarsu daga yarjeniyoyi marasa adalci da kasashen yammacin duniya suke tursasa musu wajen kullawa. Amma ita kasar Sin ta tallafawa kasashen Afirka ta fannoni da dama da suka hada da tattalin arziki, kasuwanci, ilimi, horar da kwararru, harkokin noma da sauransu ba tare da gindaya wasu sharuda ba. Wannnan ya kara karfafa gwiwar kasashen Afirka wajen dawowa daga rakiyar yammacin duniya.
Hakika, kasata Nijeriya na kan gaba cikin kasashen da suka ci gajiyar shirin kwaskwarimar tattalin arziki na kasar Sin tun daga kan kayan amfani na yau da kullum kamar wayoyin salula, kayan laturoni, da baburan hawa, hajojin tufafi, har zuwa gine ginen gadoji da kuma farfado da harkar sufurin jiragen kasar Nijeriya.
Ba shakka, ina cike da imanin cewa, yayin da tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba habaka, haka nan al'ummar Sinawa da sauran kasashen duniya za su ci gaba cin moriyar wannan bunkasa sannu a hankali. Fatana shi ne dangantaka tsakanin kasashen Afirka da Sin ta ci gaba da habaka.
Na gode.
Mai sauraronku a yau da kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Shugaban kungiyar
Great Wall CRI Listeners Club
Tianjin, China