in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawara mai kyau daga Alhaji Ali Kiraji Gashua
2018-12-17 21:16:02 cri
Salamu Alaikum!. Hakika mun ji dadi da kuka nuna mana cewa kuna yin aikinku ne dan jin dadin mu masu sauraro kana mun ji dadi da kuka bukaci jin shawarwari daga mu masu sauraronku. Agaskiya wannan damar da kuka ba mu ta zo akan gaba, wato ta zo ne dadai lokacin da muke da shaukin gabatar muku da shawarwari masu amfani dan ku kara kyautata aikinku na wayar da kan jama'a akan batutuwan da suka jibanci kasar Sin da kasashen duniya, masamman ma kasashenmu na Afirka masu tasowa.

A bangaren shafinku na internet yakamata ku dunga sabunta abubuwa da kuka sa a filinku na Zumunta a kafa take. Domun sau da yawa, kuna barin wani abu ko labari ko wani shiri da kuka saka ya jima ba ku sabunta ba. Misali, sanarwar gasar kacici-kacici da kuka sa a shafin yana daukan lokaci ba ku sabunta ba. Haka nan idan mai sauraro ko mai karatu a shafinku na facebook ya yi tsokaci a duk wani labari da kuka sa a shafin ba kwa maida murtali, sai kawai ku kawar da kai. Domun maida murtali ga mai sauraro ko mai karatu a shafinku na facebook zai kara mana kwarin guiwar ci gaba da maida hankali ga duk wani labari ko sharhi da kuka sa a shafinku na facebook. Domun na lura cewa, sau da yawa idan muka tsokaci ko muka nemi karin bayani a wani abu da kuka saka shafinku na facebook ba kwa yi mana reply.

A bangaren shirye-shiryenku na Radio yana da kyau ku dunga sabunta tsohon shirinku na Koyan sinanci. Domun a cikin shekaru masu yawa maimaitawa kuke yi, wato ba ku samar da sabbin darusa ba. Domun yin hakan, ya katse hanzarin mu masu sauraro wajen samun ci gaba da koyan harshen sinanci. Domun har yanzu muna koyan yadda ake gaisuwa(ni hao ma) da kuma yadda ake yin kidaya da dai sauransu. Haka nan, yana da kyau ku ci gaba da sabunta sharinku na Shafa labari shuni wanda tsohuwar ma'aikaciyarku malama Fatimah Inuwa Jibral take gabatarwa. Domun a kullum maimaici kuke sakawa mana. Haka nan yana da kyau ku dunga kiran masu sauraronku a layin waya kuna jin ra'ayinsu adangane da wani abu muhimmi da suka jibanci kasar Sin da kuma alakar Sin da Afirka.

Yana da kyau idan mai sauraro ko mai karatu yayi tsokaci akan wani labari ko wani batu da kuka daura a shafinku na facebook ku dunga zabar masu ma'ana daga cikin ra'ayoyi ko tsokaci da masu sauraro suka yi a shafin kuna karantowa a cikin labaran duniya da kuma a wani shirinku. Yin hakan zai kara zarafi ga masu sauraro da kuma masu bibiyarku a shafinku na facebook.

Kana yana da kyau ku dunga gabatar da gasar kacici-kacici ga masu sauraro da kuma masu bibiyarku a shafinku na facebook kamar yadda kuka saba yi a shekarun baya. Domun shirya gasa akai-akai ga masu sauraro, zai kara wayin kai sosai ga masu sauraro adangane da kasar Sin.

Banda wannan, yana da kyau ku kara daukan sabbin matakan yin gyare-gyare a fannin kara karfin sautin gidan Rediyonku na Cri masamman ma a sashin Hausa. Domun yau kimanin fiye da shekaru 10 a baya, mu masu sauraro muke fama da rashin karfin sautin muryar gidan Rediyonku. Domun kara karfin sautin zai kara wa mai sauraro zarafin fahimtar shirye-shiryenku yayinda kuke gabatar da shirye-shiryenku.

Kazalika ku samar da wani saban wakilinku a birnin Abuja wanda zai dunga hada muku rahoto daga taraiyar Nigeria. Amma rashin wakilinku a taraiyar Nigeria ya rage tagomashin Cri Hausa a taraiyar Nigeria ta fannin samun rahoto daga taraiyar Nigeria da dumi-duminsa.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China