in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sako daga malam Tijjani Musa Tijjani mai taken "mulkin mallakar kasar sin a afrika"
2018-06-22 10:47:57 cri
Kwanan baya, mun sami sako daga malam Tijjani Musa Tijjani, inda ya bayyana cewa, "kasar Sin ta shigo afrika ne domin ta musu mulkin mallaka kuma ta kwashe ma'adinai da kuma albarkatun kasashen Afrika. babu wata moriyar da kasashen afrika suke samu daga china. kayayyakin da kasar sin take kaiwa kasar afrika bata su da inganci."

Malam Tijjani Musa Tijjani, daga farko dai, mun gode maka kwarai sabo da ka aiko mana wasika, kuma ka gaya mana ra'ayinka game da huldar dake tsakanin kasarku da kasarmu. Amma a ganinmu, ra'ayinka ba daidai yake ba, hadin gwiwa da mu'amalar da kasar Sin take yi da kasashen Afirka, ciki har da kasarku Najeriya, ba shi da alaka ko kadan da batun mulkin mallakar da yammacin kasashen duniya suka taba yi a kasashen Afirka. Da farko, ma'anar mulkin mallaka ita ce yin mulkin siyasa, da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe, da kuma kwashe moriyar tattalin arziki na sauran kasashe.

Amma a fannin siyasa, kasar Sin ba ta taba tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba. Sa'an nan, a fannin tattalin arziki, kasar Sin ba ta fatan kwashe moriyar tattalin arziki na kasashen Afirka ba. Kullum, kasar Sin na jaddada cewa, yin hadin gwiwa da kasashen Afirka domin cimma moriyar juna, da kuma samun ci gaba tare, shi ne burin da ta sanya gaba.

Bugu da kari, ana gudanar da harkokin ciniki da na zuba jari bisa shawarwarin da Sin da Afirka suka yi, wadanda dole ne suka samu amincewa daga bangarorin biyu, shi ya sa, bai kamata a ce, kasar Sin tana mulkin mallaka a kasashen Afirka ba.

Haka zalika, kasar Sin tana gudanar da ayyukanta bisa tsarin mu'amalar tattalin arziki na duniya.

A halin yanzu, wasu mutane daga kasashen duniya sun riga sun gane cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka zai ba da gudummawa kan bunkasuwar kasashen Afirka a nan gaba, sabo da Sin ta ba da taimako matuka wajen warware matsalolin kasashen Afirka. Lamarin da ya sa, dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu ta ci gaba da samun bunkasuwa a shekaru baya bayan nan. Alal misali, kamfanonin kasar Sin na taimakawa kasarku shimfida wasu layukan dogo da hanyoyin mota da yawa, da kuma gina madatsar ruwa, inda suka samar da guraban aikin yi da yawa ga mutanen kasarku. Ka ce, kasar Sin ta kwashe ma'adinai da albarkatu daga kasarku, wannan ba gaskiya ba. Alal misali, a kasarku, makamashi mafi yawa kuma mafi muhimmanci shi ne man fetur, amma yawan man fetur da kasar Sin ta samu daga kasarku ya yi kadan. Bisa alkaluman da kamfanin NNPC na kasarku ya bayar kwanan baya, a shekarar 2017, kasar Indiya ce take kan gaba wajen samun man fetur daga kasarku, wato yawan gangunan da ta samu daga kasarku ya kai miliyan 131, sannan kasar Amurka tana biyo bayanta, wato ta samu ganguna miliyan 94, kasar Spaniya ta samu ganguna miliyan 66, kasar Indonesiya ta samu gangunan miliyan 24, amma kasar Sin ta samu ganguna miliyan 5.77 kawai bayan Holland, Faransa, Afirka ta kudu, Canada, Togo, Kwadivwa, Brazil da Argentina. Bisa wannan alkalumai, ko za ka iya ce kasar Sin na kwashe albarkatun kasarku? Ko ba ta biya kudin man fetur na kasarku ga kamfanin NNPC?

Sannan ka yi maganar kayayyaki marasa inganci, wannan laifi ne na 'yan kasuwar kasarku dake ba da odan yadda suke so a sarrafa musu kayayyaki. Batun ingancin kayayyakin kasar Sin ya kamata ka duba layukan dogo da sauran gine-ginen da ta yi a kasarku.

Malam Tijjani Musa Tijjani, muna fatan za ka iya ci gaba da aiko mana wasiku, amma muna fatan za ka iya ba da ra'ayinka bisa hakikanin halin da ake ciki.

Mun gode maka kwarai da gaske.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China