in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iyaye mata masu kiba su kan haifi jarirai masu kiba
2018-05-13 14:58:50 cri

Kwanan baya, wata mujallar ilmin likitanci ta kasar Amurka ta ilmin jinyar kananan yara, ta kaddamar da wani sakamakon sabon nazari dake nuna cewa, mai yiwuwa ne masu juna biyu da ke fama da matsalar kiba su haifi jarirai masu kiba.

A kan kira jarirai sabbin haihuwa wadanda nauyinsu ya wuce kilogiram 4 "jarirai masu kiba". Masu nazari daga hukumar nazarin kiwon lafiya ta kasar Amurka da dai makamantansu, sun tantance hotunan masu juna biyu fiye da dubu 2 da dari 8 da aka dauke su ta hanyar Ultrasound, da kuma sauran bayanai masu nasaba da hakan. Wadannan masu ciki sun hada da masu kiba 443, wadanda mizanin BMI dinsu ya zarce 30, da kuma masu juna biyu fiye da dubu 2 da dari 3, wadanda mizanin BMI dinsu ya wuce 19, amma bai wuce 30 ba. Mizanin BMI, mizani ne na awon nauyin mutum a kilogiram a raba da tsayin mutum a mita sikwaya. A kan yi amfani da mizanin a duk fadin duniya. Yawancin mutane suna ganin cewa, idan mizanin BMI ya wuce 25, nauyin jikin mutum ya wuce misali. Idan mizanin ya wuce 30, to mutumin yana kan sahun masu kiba.

Sakamakon tantancewar ya shaida cewa, tun daga mako na 21 da mata masu kiba suka kai bayan samun ciki, kashin cinyar 'yan tayi na masun kiba, da kuma kashin hannunsu daga gwiwa zuwa kafada da suka fi na takwarorinsu na marasa kibar tsawo. Ban da haka kuma, matsakaicin nauyin jikin jarirai sabbin haihuwa da masu kibar suka haifu ya fi na takwarorinsu wadanda masu juna biyu marasa kibar suka haihu yawa har da giram kusan 100.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, jarirai sabbin haihuwa su kan fuskanci karuwar yiwuwar karyewar kashi yayin da aka haife su, da kuma haifuwarsu ta hanyar yin tiyata. Sa'an nan kuma, iyayensu mata su kan fuskanci barazanar zubar da jini bayan haihuwa. Har ila yau nazarce-nazarcen da aka yi a baya sun shaida cewa, jarirai masu kiba sun fi saukin fama da matsalar kiba, da kamuwa da cututtukan zuciya, da na magudanar jini bayan da suka girma.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, nazarinsu ya jaddada muhimmancin yadda mata suke tabbatar da daidaiton nauyin jikinsu kafin sun samu ciki. Ya zuwa yanzu, masu nazarin ba su san dalilin da ya sa mata masu kiba su kan haifi jarirai masu kiba ba tukuna. Yanzu sun kiyasta cewa, watakila dalilin da ya sa hakan shi ne, domin mata masu kiba sun fi saukin fama da matsalar sinadarin Insulin, ta yadda da wuya su yi amfani da sinadarin wajen rage yawan sukari da ke cikin jininsu. Don haka akwai yawan sukari a cikin jininsu, lamarin da yake kara girman jariransu fiye da kima. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China