lafiya1814.m4a
|
Wani sabon nazari ya shaida cewa, shan kananan sinadaran gina jiki yayin da iyaye mata suka samu ciki, yana iya inganta basirar yaransu, ta yadda za su fi takwarorinsu nuna hazakar karatu a lokacin da shekarunsu suka wuce 9 amma ba su kai 13 a duniya ba.
Wannan nazari da aka gudanar a kasar Indonesia ya yi nuni da cewa, muhimman batutuwan da suke yin tasiri kan basirar yara su ne, kyaun muhallin da ake renonsu, da farin ciki da iyayensu mata suke ciki, da ilmi mai zurfi da iyayensu suka samu. Nazarin ya gano cewa, kyawun muhallin da ake renon kananan yara yana yin babban tasiri kan ci gaban kwakwalwarsu, da kuma yadda basirarsu ke kasancewa baki daya.
Daga shekarar 2012 zuwa ta 2014, masu nazarin sun yi bincike kan kananan yara 'yan kasar Indonesia kusan dubu 3, wadanda shekarunsu suka wuce 9 amma ba su kai 13 a duniya ba. Iyayensu mata kuma sun taba shiga wani gwaji a baya, inda aka kwatanta amfanin kananan sinadaran gina jiki ko Folic Acid kan masu juna biyu.
Sakamakon nazarin ya shaida cewa, idan masu juna biyu sun sha kananan sinadaran gina jiki, hakan na sa basirar yaransu ta wuce zaton mutane. Alal misali, yaransu sun fi takwarorinsu nuna hazakar karatu saboda sun iya rike abubuwa, ba su mantuwa. Yadda kananan yara suke rike abubuwa, ba su mantuwa, yana da muhimmanci matuka a fannonin karatunsu, da zaman rayuwarsu ta yau da kullum, kana kuma yana da nasaba da fasahohinsu na yin magana, da karanta littattafai, da buga tafireta, da kidayar abubuwa, da tuka mota da dai sauransu.
Abun da ya fi ba masu nazarin mamaki shi ne kwarewar fahimtar kananan yara, tana da nasaba da muhallin da ake renonsu, yayin da suke kasancewa a matsayin jarirai.
Ko da yake yadda masu juna biyu suke cin abubuwa masu gina jiki, da nauyin jikin sabbin haihuwa bai kai yadda ya kamata ba, da haifi jarirai da wuri, da kuma idan jikin jariri bai yi girma yadda ya kamata ba, suna kawo illa ga hazakar fahimtar kananan yaran, amma illar da suke haifarwa ba ta kai illar da muhallin yake haifarwa ba.
Batutuwan da suka shafi muhallin da ake renon jarirai sun hada da yanayin iyali, ko iyaye mata dake cikin bakin ciki, da matsayin iyaye ta fuskar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa, da kuma ilmin da suka samu da dai sauransu.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, shirye-shiryen kiwon lafiyar al'umma da ake gudanarwa a yanzu, ba su isa ba wajen kyautata hazakar kananan yara daga dukkan fannoni. Kana kyautata muhallin zaman al'ummar kasa shi ma yana da muhimmanci. (Tasallah Yuan)