in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shayar da jarirai nonon iyaye mata cikin watanni 2 yana iya rage barazanar mutuwar su ba zato ba tsammani da 50%
2018-04-23 14:28:04 cri

Wani sabon nazari ya shaida cewa, shayar da jarirai nonon iyayensu mata cikin watanni 2 na farko na rayuwar su, yana iya rage barazanar mutuwar jariran ba zato ba tsammani da kashi 50 cikin dari. Kuma haka lamarin yake ga jarirai wadanda aka shayar da su nonon iyayensu mata da kuma garin madara.

Masu nazari daga jami'ar Virginia ta kasar Amurka da sauran hukumomin nazarin sun tantance bayanan da aka samu daga manyan nazarce-nazarcen kasa da kasa guda 8, wadanda suka shafi mutuwar jarirai fiye da dubu 2 da dari 2 ba zato ba tsammani, da kuma jarirai masu koshin lafiya kusan dubu 7.

Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, ko da yake ana bin al'adu iri daban daban a kasashen duniya, amma bayanan kasa da kasa sun nuna cewa, muddin an dauki watanni 2 ko fiye da haka ana shayar da jarirai nonon iyayensu mata, hakan zai rage barazanar mutuwar jarirai ba zato ba tsammani. Amma jariran da ba su dauki watanni 2 suna shan nonon iyayensu mata ba, ba za su iya cin irin wannan gajiya ba.

Ina dalilin da ya sa shayar da jarirai nonon iyayensu mata ke iya rage barazanar mutuwar su ba zato ba tsammani? Masu nazarin sun yi hasashen cewa, watakila nonon iyaye mata yana iya kyautata karfin jarirai na kariyar jiki, ko kuma ya sauya hanyar da jariran suke bi wajen yin barci.

Idan an dauki watanni 2 zuwa 4 ana shayar da jarirai nonon iyayansu mata, hakan zai rage barazanar mutuwar su ba zato ba tsammani da kashi 40 cikin dari. Idan an tsawaita lokacin zuwa watanni 4 zuwa 6, hakan zai rage barazanar da kashi 50 cikin dari. Idan an tsawaita lokacin zuwa watanni fiye da 6, hakan zai rage barazanar da kashi 64 cikin dari.

Yanzu haka wasu hukumomi sun ba da shawarar cewa, kamata ya yi iyaye mata su dauki watanni a kalla 6 suna shayar da jariransu nononsu.

Babu bambanci a tsakanin shayar da jarirai nonon iyayensu mata da kuma shayar da jarirai nonon iyayensu mata da kuma garin madara tare, a fannin rage barazanar mutuwar jarirai ba zato ba tsammani, lamarin da ya kasance labarin da ya iya faranta ran iyaye mata, wadanda suke shayar da jarirai nonon iyayensu mata da kuma garin madara tare.

Ma'anar mutuwar jarirai ba zato ba tsammani ita ce jarirai wadanda ga alama suke cikin koshin lafiya su mutu ba zato ba tsammani, musamman ma a lokacin da suke barci. Mutuwar jarirai ba zato ba tsammani, wani muhimmin sanadi ne da ke haifar da mutuwar jariran da shekarunsu ba su kai 1 a duniya ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China