in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila abinci mai yaji na iya taimakawa wajen rage kiba
2018-03-27 06:30:33 cri

Kwanan baya, jami'ar jihar Arizona ta kasar Amurka ta kaddamar da sakamakon sabon nazari dake cewa, sinadarin Capsaicin yana taimakawa wajen sarrafa sinadaran jikin dan Adam, don haka, watakila abinci mai yaji zai taimaka wajen rage kiba.

Yayin da masu nazarin suke zantawa da manema labaru, sun bayyana cewa, bayan da suka gudanar da bincikensu ta hanyar kwatantawa da kuma aunawa,a karon farko an gano alakar kai tsaye a tsakanin sinadarin Capsaicin da kuma yawan sinadaran dake jikin dan Adam. Kana kuma, dalilin da ya sa watakila abinci mai yaji zai iya taimakawa wajen rage kiba shi ne, domin sinadarin yana bukatar amfani da karfi a maimakon danne sha'awar mutane ta cin abinci.

Masu nazarin sun gudanar da binciken kan baligai masu koshin lafiya 40 wadanda matsakaicin shekarunsu ya kai 28 a duniya. Wadannan baligai ba su sha magani mai sinadarin Bitamin ko kumu wasu magunguna ba, kana kuma an bukace su kada su ci abinci sa'o'i 4 kafin a gudanar da binciken, sa'an nan su kauce wa yin aikin karfi da motsa jiki na matsakaicin karfi ko fiye da haka sa'o'i 12 kafin a fara binciken. An gudanar da binciken sau biyu kan wadannan mutane. Da farko, an bukace su sha magani mai kunshe da sinadarin Capsaicin miligiram 2, daga baya kuma an bukace su sha wani sinadarin da ba shi da wani tasiri ga lafiyarsu a lokacin da ake gwajin amfanin sinadarin na Capsaicin.

Wadannan mutane masu koshin lafiya sun ci abincin da aka samar musu bisa karfin da suka bata yayin da suka huta, ba sa motsi jiki. Sa'an nan an auna yawan sinadaran da jikinsu ya sarrafa a bayan sa'a daya, sa'o'i 2, sa'o'i 3 daya bayan daya. Sakamakon nazarin ya shaida cewa, bayan da aka sha maganin sinadarin na Capsaicin, a kan kona Calorie 130 a matsakaicin karfi da aka yi amfani da shi a ko wace rana, yayin da idan an sha wani sinadarin da ba shi da wani tasiri ga lafiyar jiki a lokacin da ake gwajin amfanin sinadarin na Capsaicin, to, a kan kona Calorie 8 a matsakacin karfi da aka bata a kowa ce rana.

Amma duk da haka, masu nazarin sun yi gargadi da cewa, sinadarin na Capsaicin, ba magani ba ne na rage kiba. Idan ana son rage kiba, akwai bukatar tsara cikakken shirin kula da lafiya, wanda ya kunshi yadda ake ci abinci ta hanyar kimiyya, da kuma motsa jiki yadda ya dace. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China