Ganawar shugabannin kasashen Sin da Kamaru a ranar juma'a 23 ga watan mayun shekara ta 2018 a birnin Beijing na kasar Sin. A yayin ganawar shugaban kasar China shehun malami Xi Jinping ya yi tsokaci tare da yin bitar yadda kasashen 2 suka gudanar da yin mu'amula da juna ta fannin diplomasiyya, kasuwanci, hadin guiwa bisa manyan tsare-tsare da kuma musayar al'adu a cikin shekaru 47 da kafuwar huldar jakadanci a tsakanin kasashen 2.
Babu shakka, wannan ganawa da shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Kamaru mr. Paul biya, na kara samun ilmi da wayin kai adangane da huldar jakadanci dake akwai tsakanin kasar China da kamarun. Muna fata wannan ziyara da shugaba Paul biya ya kai a kasar China, za ta kara yaukaka huldar jakadanci dake tsakanin bangarorin 2, ta yadda za su kara samun zarafin kara zaburar da huldar diplomasiyya a tsakaninsu bisa sabbin matakan yin hulda da juna ta fannin kasuwanci, jakadanci, musayar al'adu, hadin guiwa da karuwar cudanya da juna ta fannin manyan aiyukan ci gaba bisa manyan tsare-tsare dan amfanuwar kasashen China da Camaroon da kuma bada zarafi ga al'ummomin kasashen ta fannin cin moriyar huldar da kasashen 2 suka kulla a cikin shekaru 47.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.