Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa na CRI suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya. Bayan haka, ina farin cikin shaida muku cewa na samu sauraron sharhin da ku ka gabatar ta shafinku na yanar gizo, dangane da alkaluman da kukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar ranar 18 ga watan Janairu, dake bayyana irin bunkasar da tattalin arzikin kasar Sin ya samu bisa ma'aunin GDP a shekarar 2017 wanda ya kai kashi 6.9 cikin dari.
Hakika, wannan kyakkyawan sakamako ne ta fannin ci gaban tattalin arziki, musamman idan an yi la'akari da cewa, sakamakon da aka samu na kashi 6.9 ya zarce hasashen da masana suka yi tun da farko. Ba shakka, tasiri wannan kyakkyawan sakamako a bayyane yake duba da yadda rayuwar al'umma a kasar Sin ke ci gaba da samun kyautatuwa sannu a hankali kamar dai yadda alkaluman hukumar suka tabbatar. Misali, batun karuwar kudin shiga na al'umma a shekarar 2017 wanda ya karu da kashi 7.3, da batun samar da aikin yi ga mutane miliyan 13 tsakanin kauyuka da birane daban daban a fadin kasar Sin, ga adadin Sinawa miliyan 129 wanda suka iya fita daga kasar Sin domin yawon bude ido a kasashen ketare, duk sun zama shaida dake tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki mai tasiri ga rayuwar al'umma. Lalle wannan abin burgewa ne kuma sakamako ne da sauran kasashe ya kamata su yi koyi da shi domin ganin rayuwar al'ummarsu ta samu kyautatuwa.
Ba shakka, ba zan manta da irin ci gaban da kasar Sin ta samu ba a shekarar bara ta 2017 a fannin kirkire-kirkire da samar da ababen more rayuwa. Misali, jirgin saman da kasar Sin ta kirkiro samfurin C919, da kaddamar da sababbin layukan dogo na jirgin kasa mai sauri, har ma da batun kaddamar da sabon jirgin kasa mara matuki wanda ya fara a aiki a kwaryar birnin Beijing cikin watan Disamban bara.
Yabon gwani ya zama dole, ina fatan tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da habaka, ina kuma fatan gudunmawar da take bayarwa a matakin kasa da kasa musamman ta fannin tattalin arziki, tsaro, ciniki da kasuwanci, da ilimi, su ma za su karu yadda ya kamata. Na gode.
Nuraddeen Ibrahim Adam
Gundumar Hexi, Tianjin