lafiya1801.m4a
|
Jaridar kwalejin ilmin abubuwa masu gina jiki ta kasar Amurka ta kaddamar da wani sakamakon nazari a kwanan baya, inda ta ce, cin kwai daya a ko wace rana yana iya rage barazanar kamuwa da shan inna da kashi 12 cikin dari.
Hadaddiyar kungiyar 'yan kasuwa masu sayar da kwai ta kasar Amurka da kwamitin kula da kwai na kasar sun ba da tallafin kudi ga cibiyar nazarin bayanai kan cututtuka masu yaduwa ta Amurka don su gudanar da wani nazari. Masu nazarin sun tantance wasu nazarce-nazarcen da aka gudanar daga shekarar 1982 zuwa 2015 dangane da alakar da ke tsakanin cin kwai da kuma kamuwa da ciwon zuciya da shan inna. Wadannan nazarce-nazarce sun shafi mutane kusan dubu 600 baki daya.
Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, babu wata alaka a tsakanin cin kwai daya a ko wace rana da kuma kamuwa da ciwon zuciya, amma cin kwai daya a kowace rana yana iya rage barazanar kamuwa da shan inna da kashi 12 cikin dari. Shan inna yana iya haddasa asarar amfanin kwakwalwa sakamakon toshewar jijiyoyin jini a kwakwalwa.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, kwai yana da abubuwa dayawa masu gina jiki, alal misali, furotin, sinadarin Antioxidant da dai makamantansu. Amma ana bukatar gudanar da karin nazarce-nazarce domin kara sanin alakar da ke tsakanin cin kwai da kuma barazanar kamuwa da shan inna.
A shekarun baya da suka wuce, likitoci da yawa sun bai wa mutane shawarar cewa, kada su ci kwai da yawa. Saboda kwai yana kunshe da sinadarin Cholesterol da yawa. Amma a watan Janairu na shekarar 2015, a cikin littafinta na ba da jagora kan cin abinci, gwamnatin Amurka ta cire kayyadewar da aka yi kan yawan sinadarin Cholesterol da mutane ke ci, littafin da gwamnatin Amurka ta kan sabunta tanade-tanadensa bayan shekaru biyar. Wato ke nan kada mutane su rika damuwa kan yawan kwan da su kan ci. Duk da haka, sabon littafin ba da jagorar ya haifar da sabani a kasar ta Amurka. Wasu hukumomi masu zaman kansu sun yi suka da cewa, sana'ar kiwon tsuntsayen gida da kwai ta kawo illa ga yadda aka sabunta littafin. Wasu daga kwamitin ba da shawara kan tsara littafin sun samu tallafin kudi daga masu sana'ar kiwon tsuntsayen gida da kwai. (Tasallah Yuan)