lafiya1740.m4a
|
Nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya sun shaida cewa, akwai wata alaka a tsakanin barazanar kamuwa da cutar daji a uwar hanji, da kuma zama wuri guda na tsawon lokaci, da shan taba, da ci jan nama da yawa. Duk da haka, sakamakon nazari da aka kaddamar a yayin taron shekara-shekara na hadaddiyar kungiyar nazarin cutar daji ta kasar Amurka, ya ba mutane mamaki kwarai da gaske.
Masu karatu, ko kun sani cewa maza masu doguwar kafa sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar daji a uwar hanji da kashi 42 cikin dari? sabanin takwarorinsu masu gajeriyar kafa?
Masu nazari daga jami'ar Minnesota ta kasar Amurka sun tantance bayanan da suka shafi masu fama da toshewar jijiyoyi, wadanda suka shiga wani nazari na tsawon shekaru 20. Masu nazarin sun yi nazari kan alakar da ke tsakanin tsayin wadannan mutane kimanin su 14,500, tsayin gangar jikinsu da tsayin kafafunsu, da kuma yawan wadanda suka kamu da ciwon sankara a uwar hanji.
Masu nazarin sun gano cewa, a cikin wadannan mutane kimanin 14,500, maza masu doguwar kafa sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar daji a uwar hanji da kashi 42 cikin dari, idan an kwatanta da takwarorinsu masu gajeriyar kafa. Barazanar kamuwa da cutar daji a uwar gaji da namiji mafi tsayin kafa da ya kai santimita 90 yake fuskanta, ta fi ta takwaransa mafi gajerta da bai wuce santimita 79 ba da kusan kashi 91 cikin dari. A cikin mata kuwa, ba a gano irin wannan alaka sosai ba.
A cikin nazarin da aka gudanar a wannan karo, tsayin kafar dan Adam, shi ne daya kacal, wanda yake da nasaba da kamuwa da cutar daji a uwar hanji. Tsayin jiki da tsayin gangar jiki ba su da alaka da kamuwa da cutar dajin.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, watakila dalilin da ya sa haka shi ne, kasancewar akwai yawan sinadaran kara girman jiki ko "Growth Hormone" masu yawa a cikin jikin maza masu tsayi. Wasu nazarce-nazarce sun shaida cewa, wani nau'in sinadarin kara girma na "Growth Hormone" kirar IGF-1, yana taimaka wa kashin dan Adam su yi girma, amma yana daya daga cikin abubuwan da suke kawo barazanar kamuwa da ciwon sankara a uwar hanji.
Nazarin da masu bincike na Amurka suka gudanar a wannan karo, ba nazari ne daya tak da ya shaida mana alakar da ke tsakanin tsayin kafar dan Adam da kuma barazanar kamuwa da cutar daji a uwar hanji ba. Domin kuwa a baya, masu nazari sun gano cewa, a cikin matan da shekarunsu suka wuce 50 a duniya, kuma ba sa yin al'adar mata, idan tsayinsu ya karu da centimita 10, barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da cututtukan daji iri-iri guda 10 tana karuwa da kashi 13 cikin dari. (Tasallah Yuan)