Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri, ina fatan baki dayan ma'aikatanku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing.
Bayan haka, ina farin cikin sanar da ku cewa yau 18 ga watan Disamba, na saurari sabon shirinku na 'Gani Ya Kori Ji' ta hanyar shafinku na yanar gizo.
Hakika, batun da malamai suka tattauna dangane da taron sha'anin yanar gizo da aka gudanar a farkon watan nan a birnin Wuzhen na lardin Zhejiang ya ja hankalina matuka. Ba shakka, a bayyane lamarin yake cewa batun yanar gizo ya riga ya zama jini da tsoka ga rayuwar al'umma ta yau da kullum. Domin ba bu wata harka ko hada-hada ta zamani da ba yanar gizo a ciki, wato harkar yanar gizo ta kawo ci gaba da alheri mai yawa ci gaban duniya da kuma kyautatuwa zaman rayuwar al'umma.
A hannu daya kuma, wasu miyagun mutane su kan yi amfani da wannan fusaha wajen cutar da al'umma ta fannoni da dama. Ina kyautata zaton wannan na daga cikin manyan dalilan da suka sa ake gudanar da irin wadannan manyan taruka na kasa da kasa, domin gano bakin zaren matsalolin da suka shafi harkar yanar gizo.
A ra'ayina, shirya wannan babban taro a kasar Sin ya dace, bisa la'akari da yadda fusahar ta samu gagarumin ci gaba a kasar. Domin kamfanin hada hadar ciniki ta yanar gizo mafi girma a duniya wato Alibaba yana kasar Sin. Ina fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu dangane da irin wadannan manyan taruka na kasa da kasa, domin akwai bukatar a tsaftace harkar fusahar yanar gizo cikin gaggawa duba da yadda rayuwar al'ummar duniya ken neman dogara kacokan kanfusahar yanar gizo. Na gode.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
birnin Tianjin, China