in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila tiyatar rage kiba za ta kara barazanar kashe kai
2017-10-23 06:36:45 cri

Yau akwai wani abu da dole ne wadanda suke sha'awar yin tiyata domin rage kiba su sani! Wani sabon nazari ya shaida mana cewa, ko da yake irin wannan tiyata ya na iya rage kiba da yawa, amma mai yiwuwa ne barazanar kashe kai ko kuma jikkata kai a sassan jiki za ta karu da kashi 50 cikin dari.

Masu nazari na kasar Canada sun kaddamar da rahoton nazarinsu a kwanakin baya inda suka ce yawancin masu fama da mummunar matsalar kiba su kan jikkata kansu a sassan jiki, ciki hada da yunkurin kashe kansu. Amma a baya ba a san illar da tiyatar rage jiki kan haifar kan wadannan mutane ba. Saboda haka, sun tantance rahotannin tarihin jinyya na masu fama da mummunar matsalar kiba fiye da dubu 8 da dari 8 na shekaru 3 kafin a yi musu tiyatar rage kiba, da kuma na shekaru 3 bayan da aka yi musu tiyatar rage kiba.

Nazarinsu ya shaida cewa, a cikin shekaru 3 bayan da aka yi wa wadannan masu fama da mummunar matsalar kiba tiyatar rage kiba, wasu 111 ne aka kai su asibiti cikin gaggawa sau 158 saboda sun jikkata kansu. Ko da yake busu da yawa, amma barazanar kai su asibiti cikin gaggawa saboda sun jikkata kansu ta karu da kashi 54 cikin dari, in an kwatanta da barazanar da suka fuskanta kafin a yi musu tiyatar.

Har ila yau kuma, masu nazarin na kasar Canada sun gano cewa, wadanda suka jikkata kansu sun fi zabar hanyar shan magani fiye da kima da gangan don kashe kansu.

A cikin rahoton nazarinsu, masu nazarin sun yi bayani da cewa, munanan abubuwa marasa kyau da suka faru kan wadannan masu fama da mummunar matsalar kiba sun raunana amfanin da tiyatar rage kiba take da shi. Nazarin da suka gudanar ya tunatar mana da cewa, ana bukatar zurfafa nazari kan dalilin da ya sa suke kara jikkata kansu bayan da aka yi masa tiyatar rage kiba, da kuma yadda za a yi rigakafin irin wannan barazana. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China