Tare da fatan baki dayan ma'aikatan ku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya a nan birnin Kano.
Ina mai cike da farin ciki yayin rubuto mu ku wannan wasika domin na bayyana jin dadi na dangane da yadda gidan rediyon CRI ya ke kokari wajen zamanantar da tsarin watsa labarai daidai da yadda zamani ke tafiya. Kamar yadda a ranar Jumu'a 31 ga watan Maris mu ka shaida yadda CRI ya kaddamar da wasu sabbin manhajoji 3 wato ChinaNews, da ChinaRadio da kuma ChinaTV duk domin a kara kyautata harkar wata labarai da sauran shirye shiryen gidan rediyon CRI.
Kodayake, ba a riga an fayyace cewa ko akwai harshen Hausa cikin harsunan da wannan sabuwar manhaja ta kunsa ba, amma ina fatan akwai harshen na Hausa. Idan kuwa haka lamarin ya kasance, to mu masu sauraro kakar mu ta yanke saka, domin CRI Hausa ya samar wa masu sauraron sa hanya mafi sauki ta zamani wacce za su rika sauraron shirye shirye kai tsaye ko kuma bayan wasu 'yan sa'oi kadan a saurari maimaici.
Wannan yana da muhimmancin gaske duba da cewa, wayoyin salula wanda manhajar ChinaRadio za ta yi aiki a kai na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a rayuwar al'umma ta yau da kullum.
Daga karshe, ina fatan CRI Hausa zai yi cikakken bayani dangane da wannan manhajar da kuma yadda take aiki. Na gode.
Mai sauraron mu a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Shugaban kungiyar
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria