Yayin da taruka biyu na NPC da CPPCC ya kawo karshe a makon da ya gabata, batun karfin tattalin arzikin kasar Sin da yadda zai ci gaba da yin tasiri a kasashen duniya ya mamaye galibin abubuwan da aka tattauna a tarukan.
Gaskiyar lamari shine, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfi, sannan kuma yana da tasiri sosai bisa ga kiyasin da masana suka yi. Kasashen duniya da dama suna amfana daga taimakekeniya da gudunmuwar da sukan samu daga kasar Sin ta bangarori da yawa.
Muna iya cewa, karfin tattalin arzikin kasar Sin, duk kuwa da nauyi daban-daban dake kan kasar, zai iya habaka sosai cikin wasu lokuta nan gaba ba tare da samun tangarda ba.
Ina taya kasar murna da wannan bunkasa. Allah Ya taimaka.
Naku,
Salisu Muhammad Dawanau
Abuja, Najeriya