Hakika shawarwari da jawabai da gyare-gyaren da wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) da membobin komitin bada shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin(CPPCC) suka gabatar wa gwamnatin kasar Sin dan kara kyautata harkokin mulki da kuma inganta zaman rayuwar jama'ar kasar Sin. Bisa wannan, muna taya gwamnatin kwaminis ta kasar Sin bisa nasarar bude tarukan 2 da kuma nasarar rufe tarukan biyu lafiya kalau. Amma batutuwan da suka fi burgeni su ne kamar haka, matakan yaki da cin hanci da kuma matakan yaki da talauci da fatara a tsakanin jama'ar kasar Sin da kuma yadda shawarwarin da aka gabatar suka fi bada muhimmanci ga inganta rayuwar jama'ar kasar Sin da kuma yaki da ta'addanci da kuma matakan da aka dauka na bunkasa fannin tattalin arzikin kasar Sin. Kana yadda shugaban kasar Sin ya gana da wakilan kabilun kasar Sin a taruka biyu da aka kammala a shekarar 2017.
Muna fata matsayar da aka cimma a tarukan 2 za su haifar da sakamako mai inganci da nagarta ga kasar Sin da jama'ar kasar Sin da ma kasashenmu na Afirka masu tasowa.
Daga Alhaji Ali Kiraji Gashua,
Tarayyar Najeriya.