lafiya1705.m4a
|
A kan ce, mu mata mun fi maza samun tsawon rai. Kwanan baya masu nazari daga reshen jami'ar Alabama ta kasar Amurka da ke Birmingham, sun kaddamar da wani sakamakon nazari da suka gabatar, wanda ke cewa watakila bambancin tsawon rai ba shi da tasiri cikin sauran halittu, kamar yadda yake tsakanin mu 'yan Adam maza da mata.
A cikin bayanin ilimi da suka wallafa, masu nazarin sun nuna cewa, yawancin mata sun fi maza nuna fifiko a fannin rayuwa a duniya, wato ke nan, mata sun fi maza samun tsawon rai. Sai dai kuma ba a gano irin wannan bambanci cikin sauran halittu ba.
Masu nazarin sun kara da cewa, ba su san dalilin da ya sa mata suka fi samun tsawon rai ba. Abu mai ban sha'awa shi ne ya zuwa yanzu, 'yan Adam ba su gudanar da wani babban nazari a kan wannan fanni ta fuskar kimiyyar binciken halittu ba tukuna.
Ko da yake ba a san dalilin da ya sa mata suka fi samun tsawon rai ba tukuna, amma masu ilmin kimiyya sun samu wasu abubuwa na shaidu dangane da lamarin.
Rumbun adana bayanan mutuwar dan Adam, wani shiri ne da masu ilmin kimiyya daga kasashen Amurka da Jamus suka gudanar cikin hadin gwiwa, a kokarin binciken tsawon ran dan Adam. Rumbun ya tanadi bayanan da ke shafar tsawon ran mata da maza daga kasashe 38. Alal misali, ya fara da tanadar bayanai a kasar Sweden daga shekarar 1751, yayin da ya fara a kasar Faransa daga shekarar 1816.
Masu nazarin sun bayyana cikin bayanin ilminsu cewa, a cikin wadannan kasashe 38, bayanan na ko wace shekara sun shaida cewa, tsawon rai da mata suke sa ran samu ya fi wanda maza suke sa ran samu.
Ban da haka kuma, a duk lokacin da ran wani ko wata, ko shekarunsa ko shekarunta suka kai 5 a duniya, ko suka kai 50 a duniya, to, mata sun fi nuna fifiko wajen kara ci gaba da rayuwa, lamarin da ya fayyace dalilin da ya sa mata, suke samun rinjaye a cikin wadanda shekarunsu suke wuce 100 suna raye.
Har ila yau, masu nazarin sun gano cewa, kwarewar mata wajen yaki da mutuwa ya fi ta maza nagarta. Masu nazarin sun yi bayanin cewa, ko da yake mata sun fi maza samun tsawon rai, amma lafiyar yawancin baligai mata ba ta kai ta baligai maza ba. Alal misali, baligai mata su kan samu saukin fama da amosanin gabbai, da lalacewar kashi da dai sauransu, lamarin da shi ma yake daya daga cikin bambancin jinsi da ya fi ba mutane mamaki. (Tasallah Yuan)