Kasar Sin da Nigeria sun samar da yarjeniyoyi da dama akan fannoni daban daban a cikin shekarru 46 da suka gabata wadanda suka hada da,
1. Samar da bashin da ba ya da ruwa domin bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, tare da samar da ci gaban masana'antun kasar Nigeria da samar da harkar makamashi mai tsabta da tallafin aikin gona ga dukkanin fadin kasa baki daya.
2. Kasar Sin ta bude kofa ga dukkanin al'ummar Nigeria domin samar da ci gaban kasuwancin 'yan kasa domin ci gaban tattalin arzikin kasashen biyu.
3. Kamfanonin kasar Sin sun sami taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasar Nigeria ta fanin samar da gine gine na zamani wadanda suka hada da samar da titunan mota, layin dogo, gadojin mota, filayen jiragen sama da na ruwa, da gina manyan gidaje da hotel hotel tare da samar da kayayyakin more rayuwa a ko'ina a fadin kasa.
4. Kasar Sin ta samar da gurabun samar da ilimi a kasar Sin ga al'ummar Nigeria tare da bayar da tallafi ga daliban Nigeria cikin dogon lokaci tare da samar da tallafin ilimi a cikin gidan Nigeria.
5. Kasar Sin ta samar da kafa ta yawon bude ido tsakanin 'yan Nigeria a cikin shekaru 46 da suka gabata inda mutane da dama suka sami goron gayyata domin yawon bude ido tare da fahimtar al'adun Sin a idon duniya inda masu hulda da kafar yada labarum kasar Sin wato CRI ke daukar nauyin tafiyar yawon bude ido, misalin da ni kaina na sami damar kai ziyara ta wannan hanya da sauransu.
6. Ba shakka kasar Sin da Nigeria suna samun muhimmiyar ci gaba a cikin shekarun da suka gabata tare da ci gaban tattalin arzikin kasashen cikin sauri ba shakka nuna fatar kasashen biyu za su kara samun ci gaba mai inganci fiye da yadda wadannan shekaru da suka gabata amen. Allah ya ja zamanin kasar Nigeria da kasar Sin baki daya. Ameen.
Daga mai sauraronku a ko da yaushe,
Shugaba,
Bello Abubakar Malam Gero,
Sokoto state,
Nigeria.