in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na saurari sabon shirin Gani Ya Kori Ji
2017-02-08 08:20:26 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Tare da fatan daukacin ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya a nan birnin Kano.

Bayan haka, na samu zarafin sauraron sabon shirin ku na "Gani Ya Kori Ji" na makon da ya gabata, wato Laraba 1 ga watan Fabrairu, wanda malamai Saminu Alhassan da Ahmad Inuwa Fagam suka gabatar bisa jagorancin Ibrahim Yaya.

Hakika, na ji dadin sauraron wannan sabon shiri wanda malamai suka tattauna batun bunkasar tattalin arzikin kasar Sin musamman a daidai wannan lokaci da kasashen duniya ke fuskantar kalubaloli iri daban daban wajen raya tattalin arzikin su.

Wannan maudu'i na tattalin arziki da malamai suka gabatar da sharhi a kai ya burge ni kuma ya ja hankali na sosai, domin kimanin makonni biyu kenan na aiko da wata wasika ga sashen Hausa inda na bayyana ra'ayi na dangane da yadda tattalin arzikin kasar Sin ya ke samun ci gaba duk da cewa sauran kasashen duniya ciki kuwa har da masu sukuni na fama da matsin tattalin arziki.

Kamar yadda masu iya magana kan ce, abin da ke gidan "Kaura shi ne a gidan Goje", domin ra'ayi na dake yaba wa nagartar tattalin arzikin kasar Sin ya zo daidai da na malaman wanda ba ya ga jinjina wa tsarin tattalin arzikin kasar Sin sun kara da yin fashin baki dangane da matakan tallafa wa tattalin arziki daban daban da hukumomi a kasar Sin suka dauka wanda a zahiri suka taimaka wajen hana rikita rikitar tattalin arzikin duniya yin tasiri a kan kasar ta Sin.

A halin yanzu za a iya cewa, kwalliya ta riga ta biya kudin sabulu, domin matakan da kasar Sin ta dauka na aiwatar da kwaskwarima ga tsarin tattalin arziki na sarrafa kayayyakin da masana'antu ke samarwa fiye da kima ko dogaro ga fitar da kayayyakin zuwa kasashen ketare domin samun kudaden musaya zuwa tattalin arziki dake ba da fifiko ga raya kasuwannin cikin gida tare da bunkasa fannin ba da hidima, lamarin da ya sa karfin tattalin arzikin kasar Sin ya zauna daram a kan kashi 6.7% cikin dari a shekarar 2016. Abin mamaki a nan shi ne, wannan mataki da hukumomi suka dauka bai dade ba amma ya kawo tasiri mai yawa wanda ya daga matsayin tattalin arzikin kasar Sin fiye da yadda ake zato. Dalili a nan shi ne, alkaluman da hukumomin kudi suka fitar sun nuna cewa, fannin bayar da hidima ya samar da kashi 51% na daukacin kudaden shiga na biliyoyin dalar Amurka wanda gwamnatin kasar Sin ta samu a shekarar da ta gabata.

Hakika, mahukunta sun yi tsinkaye dangane da yanke shawarar ba da muhimmanci ga kasuwannin cikin gida duba da dimbin arzikin al'umma da ya zarce biliyan 1 da miliyan 350 da kasar Sin ke da shi. Ba shakka, wannan adadi wanda ya zarce yawan daukacin al'ummar nahiyar Afirka zai taimaka wa kasar ta Sin wajen samar da wata babbar kasuwa mai tabbas wacce tattalin arziki zai iya dogaro da ita ba tare da wata matsala ba. Godiya da yabo ga shugabannin kasar Sin karkashin jagorancin JKS bisa ceto al'ummar Sinawa daga halin hannu baka hannu kwarya zuwa wata kasa ta zamani mai wadata kuma ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Dangane da haka, lalle za a iya cewa, akwai darasi mai yawa da kasashen mu na Afirka za su iya koya daga matakan sauya alkiblar tattalin arzikin da kasar Sin ke yi lokaci zuwa lokaci domin dacewa da zamani, maimakon dogaro da ciyo bashin kudade dake tattare da tulin kudin ruwa wai da sunan cike gibin kasafin kudi ko kuma samar da ababen more rayuwa. Ya kamata kasashen mu na Afirka su farka kuma su sauya tunani wajen lalube da kulle kullen nema wa kai mafita, kamar yadda kasar Sin ba ta dogaro ga kowacce kasa wajen magance wa kai matsalar tattalin arzikin da ta zamantakewa.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China