in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shawarta cin bitamin D mai microgramme 10 a ko wace rana
2017-01-22 12:12:59 cri

Wata kungiyar kwararu, ta mika wa mahukuntan kasar Birtaniya wani rahoton dake cewa, 'yan Birtaniya da yawansu ya kai kashi daya cikin 5, su na fama da karancin sinadarin bitamin D a jininsu, a don haka Rahoton ya shawarci mutanen da shekarunsu suka wuce 1 a duniya, su rika cin abinci mai sinadarin bitamin D mai microgramme 10 kowace rana, don tabbatar da ganin kasusuwa da jijiyoyi sun yi girma yadda ya kamata.

Bitamin D, wani nau'in sinadarin bitamin ne wanda yake iya narkewa cikin mai, yana taimakawa jikin dan Adam wajen shigar da sinadarin Calcium, lamarin da yake da matukar muhimmanci wajen tabbatar da kyaun kasuwan dan Adam. Idan mutum na fama da tsananin karancin bitamin D, akwai yuwar ya yi fama da matsalar lalacewar kashi da kuma ciwon Rickets. A yawancin lokuta, mutane su na iya samun shigar bitamin D ne ta hanyar shiga rana na wani lokaci, da kuma cin abinci mai dauke da shi.

kungiyar kwararrun da ta dauki shekaru 5 ta na tantance lafiyar 'yan Birtaniya, ta kuma nuna cewa, 'yan kasar su kan samu shigar bitamin D mai microgramme 3 a ko wace rana ta hanyar cin abinci da abubuwa masu gina jiki.

A Birtaniya, wadanda suka fi saukin fama da karancin bitamin D sun hada da 'yan kananan kabilu masu bakaken fata, wadanda ba sa shiga rana, da mutanen da su kan rufe jikinsu da riga dalilan addini da al'adu, da kuma wadanda ba su da isasshen lokacin shiga rana dalilin aikinsu, kamar wadanda suke aikin dare.

kwararrun sun yi bayanin cewa, ya zuwa yanzu, mutane masu yawa suna ganin cewa, shiga rana na wani lokaci, ya na iya biyan bukatun yawancin mutane ta fuskar shigar da isasshen bitamin D, amma sakamakon nazarin ya nuna cewa, ba haka ba ne. kwararrun sun bada shawarar kara shigar da bitamin D ta hanyar cin wasu abinci, kamar kara cin kifin Salmon, kifin Tuna da sauran kifaye masu kiba, da kwai da kuma gyararriyar alkama wadda aka mayar da ita tamkar karin kumallo.

Har ila yau, sun kara da cewa, yawancin mutane su na iya samun isasshen bitamin D ta hanyar shiga rana da kuma cin abinci yadda ya kamata a lokacin bazara da lokacin zafi. Amma a lokacin kaka da kuma lokacin hunturu, sakamakon raguwar lokacin shiga rana, ya zama wajibi a yi la'akari da cin abubuwa masu gina jiki domin samun isasshen sinadarin bitamin D. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China