lafiya1640.m4a
|
A kwanakin baya ne, wata kungiyar nazari ta kasa da kasa, karkashin jagorancin masana daga jami'ar Alberta ta kasar Canada ta kaddamar da rahoton nazarinta, inda aka gano cewa, kumburin da ya kewaye zuciyar dan Adam tana taimakawa wajen yin hasashen barazanar mutuwa da masu fama ciwon koda suke fuskanta a yayin da suke doguwar jinya. Idan wannan kunburi da ke kewayen zuciyarsu ya ci gaba da karuwa, to,barazanar da suke fuskanta ta mutuwa za ta ci gaba da karuwa.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, sun gudanarwa da bincike da ka a kan wasu Amurkawa 109 marasa lafiya dake doguwar jinya sakamakon ciwon koda,inda sun gano cewa, idan har girman kunburin da ke kewayen zuciyarsu ya karu da Cubic Centimeter 1, to, barazanar mutuwa da suke fuskanta za ta karu da misalin kashi 6 cikin dari. Kana kuma, idan girman kunburin da ke kewayen zuciyar marasa lafiyar ya dara matsakaicin girmansa to, yiwuwarsu ta rayuwa shekaru 5 a duniya ya kai misalin kashi 45 cikin dari. Idan kuma girman wannan kumburi ya yi kasa da matsakaicin girman kunburin, to, yiwuwarsu ta rayuwa shekaru 5 a duniya ya kai kashi 71 cikin dari.
Nazarce-nazarcen da aka yi a baya sun tabbatar da cewa, lalacewar jijiyar jini da ke cikin zuciya, alama ce ta karuwar girman wannan kumburi. Masu nazarin sun yi nuni da cewa, yin amfani da na'urar daukar hoton sassan jiki ta CT yana taimakawa wajen gano jijiyar jini da ke zuciyar marasa lafiya da ta lalace, don haka masu nazarin suka ba da shawarar cewa, wajibi ne a yiwa marasa lafiya dake doguwar jinya sakamakon ciwon koda bincike ta hanyar amfani da na'urar daukar hoton sassan jiki ta CT yayin da ake musu jinya.
Har wa yau kuma, masu nazarin sun yi gargadi da cewa, bai kamata lokitoci su yanke hukunci saboda girman kunburin da ke kewayen zuciyar marasa lafiya bisa dalilai na kiba ko kuma ramar masara lafiya ba. Saboda wasu marasa lafiya, tun asali sirara ne amma suna da kumburi a kewayen zuciyarsu, yayin da wasu marasa lafiyan kuma, masu kiba ne ainun, amma ba su da kumburi a kewayen zuciyarsu. (Tasallah Yuan)