in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yin aiki na dogon lokaci fiye da kima ya kan kara barazanar kamuwa da ciwon zuciya da na magudanar jini
2016-12-11 12:10:01 cri

A kwanakin baya ne a kasar Birtaniya wata kungiyar nazari ta kasa da kasa ta kaddamar da rahoton nazarin da ta gudanar, inda a cewarsu, idan har mutum ya kashe sa'o'i 55 ko fiye da haka a ko wane mako yana gudanar da aiki, to, barazanar da yake fuskanta ta kamuwa da ciwon zuciya da shanyewar sassan jiki zai karu.

Kungiyar nazarin, wadda ke karkashin shugabancin masana daga kwalejin jami'ar London, ta tantance bayanai iri-iri guda 25 da takwarorinsu masana suka tattara a baya, dangane da lafiyar masu aikin sa kai fiye da dubu 600 da suka fito daga kasashen Turai, Amurka da Australia, wadanda suka rika bai wa masu nazarin bayanan lafiyar jikinsu ba tare da tsayawa ba cikin shekaru 8 da rabi a kaddarance.

Sakamakon tantancewar ya shaida cewa, idan aka kwatanta su da masu aikin sa kai wadanda su kan shafe sa'o'i 35 zuwa 40 suna aiki a ko wane mako, to, masu aikin sa kai wadanda su kan shafe sa'o'i 55 ko fiye da haka suna aiki a ko wane mako su kan kara fuskantar barazanar kamuwa da ciwon zuciya, adadin da zai karu da kashi 13 cikin dari.

A fannin kamuwa da shanyewar sassan jiki kuma, masu nazarin sun tantance bayanan lafiyar al'umma iri-iri guda 17 na daban, bayanan da aka tattara daga wajen masu aikin sa kai kusan dubu 530. Matsakaicin lokaci da masu aikin sa kai suka kashe wajen bayar da bayanan lafiyarsu ya zarce shekaru 7 baki daya. Masu nazarin sun gano cewa, barazanar kamuwa da shanyewar sassan jiki da masu aikin sa kai wadanda su kan shafe sa'o'i 55 ko fiye da haka suna aiki a ko wane mako suke fuskanta, ta karu da misalin kashi 30 cikin dari, idan aka kwatanta su da wadanda su kan shafe sa'o'i 35 zuwa 40 suna aiki a ko wane mako.

Masu nazarin sun yi bayani cewa, suna bukatar zurfafa nazarinsu domin kara fahimtar dalilan da suka haddasa hakan. Amma duk da haka suna ganin cewa, mai yiwuwa dalilan da za su haddasa hakan su ne, matsalolin da wadanda su kan dauki dogon lokaci fiye da kima suna aiki suke fama da su, kamar rashin motsa jiki na tsawon lokaci, sha'awar shan giya, fuskantar babban matsin lamba a fannin aiki, da dai sauransu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China