lafiya1637.m4a
|
Masu nazari daga jami'ar ta Exeter dake kasar Birtaniya, sun kwashe shekaru 16 suna gudanar da bincike kan mutane fiye da dubu 5, sun kuma rubuta tsawon lokaci da wadannan mutane suke shafewa a zaune, da na tafiya, da na gudanar da mabambantan ayyukan karfi a zaman yau da kullum, da kuma al'adarsu ta zama a wurin aiki, da gidaje da kuma sauran wurare.
A karshe dai sun gano cewa, zama tsawon lokaci ba ya kara ko kuma rage barazanar mutuwa.
Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, ainihin dalilin da yake kara barazanar mutuwa shi ne, rashin isasshen motsa jiki, a maimakon zama tsawon lokaci. Sun ce zama tsawon lokaci, ko kuma tsaiwa cikin dogon lokaci ba tare da motsawa ba, ya kan sanya jikin dan Adam rashin amfani da karfi da yawa, lamarin da watakila ya raunana lafiyar dan Adam.
Kaza lika masu nazarin na Birtaniya sun nuna cewa, nazarinsu ya shaida mana cewa, idan ana son rage barazanar mutuwa, to, rage tsawon lokacin da ake dauka ana zaune ba shi da muhimmanci kamar yadda aka zata a baya. Amma duk da haka, idan ana da bukatar kasancewa cikin koshin lafiya, da kuma samun tsawon rai, kamata ya yi dan Adam ya kara motsa jiki a kullum.
Bayan haka kuma, jami'ar Tohoku ta kasar Japan ta sanar a kwanan baya da cewa, bayan masu nazari daga jami'ar sun yi bincike kan beraye, sun gano cewa, motsa jiki cikin dogon lokaci yana iya rage illar da ciwon koda dake biyo-bayan ciwon sukari yake haddasawa.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, sakamakon nazarinsu ya tabbatar da rawar da motsa jiki ke takawa a fannin shawo kan ciwon koda wanda ke biyo-bayan ciwon sukari. In an kwatanta hakan da yin amfani da magani, da kuma yin tiyata, motsa jiki ya fi fifiko a fannonin tsimin kudi, da kuma tabbatar da tsaron lafiyar masu fama da ciwon. (Tasallah Yuan)