in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Motsa jiki mai matukar yawa na taimakawa wajen rage barazanar mutuwa da wuri
2016-11-14 09:26:55 cri

Idan kana cikin koshin lafiya, to, ya fi kyau ka kara motsa jiki mai matukar yawa. Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Australia ya nuna cewa, motsa jiki da ya kan haddasa haki da yin gumi, suna iya rage barazanar mutuwa da wuri.

Masu nazarin sun dauki shekaru fiye da 6 suna gudanar da bincike kan 'yan kasar Australia fiye da dubu 200, wadanda shekarunsu suka wuce 45 a duniya, a cikinsu kuma, wasu fiye da 7400 sun mutu.

Masu nazari daga kwalejin ilmin kiwon lafiyar al'umma na jami'ar Sydney sun yi bayanin cewa, bincikensu ya shaida cewa, da farko dai, motsa jiki yana da matukar muhimmanci, kuma kara motsa jiki yana iya rage barazanar mutuwa da wuri. Na biyu kuma motsa jiki mai matukar yawa ya fi motsa jiki matsakaici amfani ga lafiyar dan Adam.

In an kwatanta wadanda suke motsa jiki matsakaici, a bangaren barazanar mutuwa da wuri da wadanda suke motsa jiki mai matukar yawa, kaso na biyu na da damar samun raguwa da kashi 9 cikin kashi dari zuwa kashi 13 cikin kashi dari, duk da cewa, suna cikin koshin lafiya, ko kuma wadanda suke fama da matsalar kiba ko ciwon zuciya.

To ko mene ne ma'anar motsa jiki mai matukar yawa? Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, motsa jiki mai matukar yawa shi ne motsa jiki dake haddasa karuwar yawan bugun zuciya da yawa, da haki da yin gumi, kamar hawan dutse, ko gudu, ko wasan kwallon kwando, ko wasan kwallon kafa, da rawar motsa jiki don kara lafiya a tsawon lokaci, ko ma wasan kwallon tennis, ko hawan keke cikin sauri da dai sauransu. Ban da haka kuma, daukar kaya mai nauyi, da sauran ayyukan karfi a zaman yau da kullum, su ma su na cikin irin wannan nau'i na motsa jiki mai matukar yawa.

Yanzu hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta ba da shawarar cewa, a ko wane mako, ya fi kyau a motsa jiki matsakaici na a kalla mintoci 150, ko kuma a motsa jiki mai matukar yawa na mintoci 75. Kasashen Amurka, Birtaniya, Australia da wasu kasashe sun ba da irin wannan shawara.

Duk da haka masu nazarin na Australia suna ganin cewa, ya kamata a karfafa gwiwar masu koshin lafiya da su motsa jiki mai matukar yawa. Wajibi ne a yi iyakacin kokarin kwashe mintoci a kalla 150 a ko wane mako wajen motsa jiki, lamarin da zai iya rage barazanar mutuwa da wuri. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China