#Ni da CRI# Gabatar da ra'ayin kasar Sin domin biyan bukatun masu sauraro a wurare daban daban
A watan Faburairu na shekarar 2006 ne, tashar FM ta CRI dake Nairobi na Kenya ya fara aiki a hukunce. Wannan ita ce tashar FM ta farko da gidan rediyon CRI ya kafa a ketare. Ya zuwa karshen shekarar 2015, gidan rediyon CRI ya bude gidajen rediyon hadin gwiwa 130 a ketare, da mitocin watsa shirye-shirye na hadin gwiwa 160, da ofisoshin watsa shirye shirye 26 a ketare, da kwalejojin Confucius na koyon al'adun Sinawa 15, wadanda suka biya bukatun masu sauraronmu dake ketare ta yadda za su kara fahimtar kasar Sin yadda ya kamata.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku