in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasannin bidiyon nuna karfin tuwo ba su iya rage matsin lambar da ake fuskanta ba
2016-08-15 07:14:29 cri

Sakamakon ci gaban fasaha ya sa yanzu haka ana kara raya sassan da ke cikin wasannin bidiyo, da kuma hotunan wasannin dake ciki ta yadda sukan zama tamkar na gaskiya, kana kuma ana kara kawar da bambancin da ke tsakanin zaman rayuwar yau da kullum na gaskiya, da kuma abun dake wakana cikin wasannin. Mutane masu tarin yawa suna matukar sha'awar yin wasannin bidiyo, ciki had da wasu wadanda suke yin wasannin bidiyon domin rage matsin lambar da suke fuskanta ta fuskar karatu, ko aiki, ko kuma zaman rayuwa. Duk da haka, sakamakon wani nazari da aka gudanar a kasar Faransa ya shaida mana cewa, wasannin bidiyo na nuna karfin tuwo, ba su iya taimakawa masu wasa rage matsin lambar da suke fuskanta, maimakon hakan ma masu sha'awar wasannin kan kara samun rashin sakin jiki da rashin hakuri.

Masana masu ilmin nazarin halayyar dan adam, a fannin zamantakewa daga wata jami'ar da ke birnin Grenoble a kudu maso gabashin kasar Faransa sun gudanar da wani nazari a kwanan baya, inda suka gayyaci dalibai 87 da aka bawa umarnin kar su dauki mintoci 20 suna yin wasannin bidiyon nuna karfin tuwo ko kuma takwarorinsu dangane da sauran fannoni. Daga baya masanan sun bukaci wadannan dalibai da su karanta wani bayani mai cike da abubuwan nuna karfin tuwo, tare da daukar faifai kan muryarsu. A karshe dai masanan sun tantance muryar daliban cikin kamfuta, a kokarin tabbatar da motsin rai na wadannan dalibai da kuma yanayin da suke kasancewa na tunani.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, kamar yadda aka zata a baya, in an kwatanta daliban da suka yi wasannin bidiyo dangane da sauran fannoni, wadanda suka yi wasannin bidiyon nuna karfin tuwo sun kara samun rashin sakin jiki da rashin hakuri.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, wasu mutane sukan yi wasannin bidiyon nuna karfin tuwo da zummar samun sakin jiki da rage matsin lambar da suka fuskanta, amma yin wasannin bidiyon nuna karfin tuwon, ba wani zabi ne mai dacewa ba a gare su. Wadannan wasannin bidiyon nuna karfin tuwo su kan kara samar musu matsin lamba. Haka zalika kuma, akwai wani abun da ya zama tilas mu lura da shi, wato fuskantar matsin lamba cikin dogon lokaci yana iya kawo illa ga lafiyar jikin dan Adam, yana kuma iya kara wa mutane barazanar kamuwa da ciwon zuciya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China