in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Idan masu fama da ciwon sankara suna da karin masaniya game da ciwonsu, hakan zai inganta sakamakon jinyar ta su
2016-07-21 17:20:02 cri

Kwalejin Birkbeck dake jami'ar London ta kasar Ingila, ta kaddamar da sakamakon wani nazarin ta a kwanan baya, inda a cewar binciken, kyakkyawar sanayya game da jinyar masu fama da ciwon sankara, na iya inganta sakamakon da masu fama da ciwon ka iya samu.

Masu nazari daga jami'ar sun tantance halin da masu fama da ciwon sankara fiye da dubu 10 suka kasance a ciki, inda suka gano cewa inda masu fama da ciwon suna da karin sani kan illar da ciwon sankarar su ke haifawa a fannonin aikinsu da zaman rayuwarsu, to, jinyar da suke samu za ya fi tasiri sama da jinyar da wasu da ba su da sanayya kan ciwon na su da linki 1.72. Kana kuma idan masu fama da ciwon suna da masanaiya kan nau'in ciwon da suke fama da shi, to, jinyar da suke samu za ta fi tasiri sama da jinyar wadanda ba su da sanayyar hakan da linki 1.99.

Har ila yau idan masu fama da ciwon suna da sanayya kan ciwonsu kafin a yi musu tiyata, to, jinyar da suke samu za ta fi jinyar da wadanda bas u da wannan masaniya tasiri da linki 1.9.

Masu nazarin sun yi bayanin cewa, dalilan da suka sa hakan su ne; da farko, idan masu fama da ciwon sun kara fahimtar su kan ciwon na su, to, hakan zai rage rudewar su, da matsin lambarsu sakamakon rashin tabbaci kan ciwon na su. Na biyu kuma, idan masu fama da ciwon sun san yadda za a ba su jiyya, to, za su kara tinkarar wasu matsalolin da a kan gamu da su sakamakon matakan jinya yadda ya kamata, ta yadda za su iya kyautata yadda suke gudanar da harkokin aikinsu, da zaman rayuwarsu yadda ya kamata.

Amma duk da haka, masu nazarin sun yi nuni da cewa, barin masu fama da ciwon sankara su san matsalolin da a kan gamu da su a sakamakon jinya fiye da kima, ya kan kara wa masu fama da ciwon matsin lamba a tunani, ta yadda za su iya fara nuna shakku kan yadda ake musu jinya. A karshe jinyar da ake musu ba za ta yi aiki yadda ya kamata ba. Don haka nan gaba ana bukatar gudanar da karin nazari, domin lalubo bakin zaren hanyar da za ta fi dacewa, wajen taimakawa masu fama da tsananin ciwon sankara. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China