lafiya1619.m4a
|
Wani sabon nazari da aka gudanar kan mutane masu yawa, ya shaida cewa, inganta yanayin zaman rayuwa ta hanyar da ta dace cikin dogon lokaci, ba kawai yana taimakawa wajen yin rigakafin ciwon sankarar uwar hanji ba ne, har ma yana ba da taimako wajen yawaita masu tsira da ransu bayan fama da ciwon sankarar uwar hanjin.
A baya bayan nan, wasu masu bincike na ganin cewa, kyautata yanayin zaman rayuwa ta hanyar da ta dace cikin dogon lokaci, yana taimakawa wajen rigakafin ciwon sankarar hanji, kana yana ba da taimako wajen kara yawan masu fama da ciwon sankara dake iya tsira da rayukan su. Masu nazari daga kwalejin koyon ilmin kimiyya da fasaha ta kasar Ingila sun gudanar da nazari kan masu fama da ciwon sankarar uwar hanji.
Cikin shekaru fiye da 6 da suka shafe suna gudanar da nazarin na su, a farkon sa sun rubuta bayanai dangane da lafiyar mutane fiye da dubu 500 da ke zaune a kasashe 10 na nahiyar Turai, da kuma hanyar zaman rayuwarsu. A lokacin gudanar da nazarin, wasu 3,292 daga cikinsu an tabbatar da sun kamuwa da ciwon sankarar uwar hanji.
Masu nazarin sun tsara wani tsarin kidayar maki na musamman, inda ake auna nauyin jikin maza, da al'adarsu ta motsa jiki, da abincin da su kan ci, da sauran fannonin da ke shafar hanyar zaman rayuwarsu kan ma'aunin dake tsakanin lamba daya zuwa 6. A bangaren mata kuma, an kara maki wajen "shayar da jariransu nonon uwa zalla" a cikin fannonin da aka auna, kan ma'auni tsakanin lamba daya zuwa 7. Karin maki da wata ke iya samu na nuni da karin ingancin hanyar zaman rayuwar ta ke nan.
Bayan da masu nazarin suka tantance bayanan da suka samu, kafin, da kuma bayan an tabbatar da wadanda suka kamu da ciwon sankarar uwar hanjin, sun gano cewa, wadannan mutane mata da maza idan makin da suka samu na karuwa, to, barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da ciwon sankarar uwar hanji tana ta raguwa. Har wa yau kuma, kasancewa cikin madaidaicin nauyin jiki da kuma cin yawan 'ya'yan itatuwa da kayan lambu, suna ba da taimako wajen kara damar tsira da rai ga masu fama da ciwon sankarar uwar hanjin. A cikin matan kuma, shayar da jariransu nonon uwa zalla, shi ma ya taimakawa masu fama da ciwon sankarar uwar hanjin tsira da ran su.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, sun tattara wadannan bayani ne kafin tabbatar da masu kamuwa da ciwon na sankara, lamarin da ya nuna cewa, nacewa ga zaman rayuwa ta hanyar da ta dace, yana da matukar muhimmanci. (Tasallah Yuan)