lafiya1618.m4a
|
Masu karatu, ko kun taba ganin zanzaro? Mai yiwuwa a ganinku, zanzaro, wani nau'in karamin kwaro ne kawai, kuma ya kan harbi mutane, amma a nan gaba watakila za a yi amfani da dafin sa wajen jinyar masu fama da ciwon sankara.
Kwanan baya, wani nazarin da masu bincike daga kasashen Birtaniya da Brazil suka gudanar cikin hadin gwiwa, ya shaida mana cewa wani nau'in zanzaro da ake samu a kasar Brazil yana iya samar da wani nau'in dafi, wanda a cikin sa wasu sinadarai ke iya kashe kwayoyin halitta na ciwon sankara, kuma ba su jikkata sauran kwayoyin halitta na jikin dan Adam. Don haka ana sa ran cewa, za a sarrafa irin wannan dafi don samar da sabon maganin yaki da ciwon sankara a nan gaba.
Irin wannan zanzaro sunansa Polybia paulista. Yayin da suke yi kicibis da masu kawo musu hari, su kan samar da wani nau'in dafi a wutsiyarsu domin kare kansu. Irin wannan dafi ya kunshi wani nau'in sinadari mai suna MP1, wanda ke taka rawa wajen yaki da ciwon sankara.
Bayan da masu nazari daga jami'ar Leeds ta kasar Ingila, da jami'ar Sao Paulo State ta kasar Brazil suka tantance sinadarin MP1, sun gano cewa wannan sinadari kan haifar da kananan ramuka a kwayoyin halittu na ciwon sankara, ta haka sinadaran da ke taka muhimmiyar rawa a cikin wadannan kwayoyin halittu na ciwon sankara za su malale.
A gwaje-gwajen da aka yi cikin dakin gwaji, masu nazarin sun gano cewa, irin wannan sinadari mai suna MP1, yana iya hana kwayoyin halittu na ciwon sankarar mafitsara, da na mara, har ma da ciwon sankarar jini su yi girma, ba kuma tare da sun kawo illa ga lafiyar sauran kwayoyin halittu ba.
Amma duk da haka masu nazarin sun yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu ba a san yadda sinadarin na MP1 da ke cikin dafin zanzaron ke iya zabar kwayoyin halittu na ciwon sankara ba, a maimakon sauran kwayoyin halittun da ke cikin jikin dan Adam. Watakila lamarin yana da nasaba da halin tantanin kwayoyin halittu na ciwon sankara.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, idan aka gano yadda sinadarin MP1 yake taka rawa wajen hana kwayoyin halittu na ciwon sankara, kana kuma aka tabbatar da yadda sinadarin ke aiki yadda ya kamata, ba tare da ya lalata lafiyar dan Adam ba, hakan zai iya yin amfani ga samar da sinadarin, wajen sarrafa sabbin magunguna wadanda za su fi magungunan da aka saba sha na yaki da ciwon sankara. (Tasallah Yuan)