lafiya1617.m4a
|
Nazarin ya kuma yi nuni da cewa, masu juna biyu da sukari ya yi yawa a jininsu, nan da nan su kan haifi jarirai masu kiba.
Masu nazarin sun gano cewa, idan nauyin jarirai sabbin haihuwa ya wuce misali, ko kuma nauyin su bai kai yadda ya kamata ba, lamarin kan kawo babbar barazana ga lafiyarsu, kuma akwai wata alaka a tsakanin nauyin jikinsu da barazanar kamuwa da ciwon sukari nau'I na 2. Don haka watakila kara sanin yadda nauyin jikin masu juna yake kawo illa ga nauyin jarirai sabbin haihuwa, zai taimaka wajen taimakawa masu juna biyu su kasance cikin koshin lafiya yayin da suke samun ciki, ta yadda za a rage yawan jarirai wadanda nauyin jikinsu ya wuce misali ko bai kai yadda ya kamata ba.
Masu nazarin sun tantance bayanan mata fiye da dubu 30 da kuma jariransu wadanda aka gudanar da nazari a kai a fannoni guda 18 a baya a kasashen Turai da Amurka da Australia, ciki had da tsayin masu juna biyu, nauyin su, yawan sukari da ke cikin jininsu, yawan kitsen da ke cikin jininsu,yanayin hawan jininsu da dai sauransu, da kuma sauye-sauyen kwayoyin halitta. Dukkan wadannan mata, 'yan asalin kasashen Turai ne, kuma sun haifi jariransu daga shekarar 1929 zuwa shekarar 2013.
Sakamakon nazarin ya shaida cewa, nauyin jikin iyaye mata, yawan sukari da ke cikin jininsu, da yanayin hawan jininsu kan haifar da illa ga nauyin jariransu. Ko da yake yawan kitsen da ke cikin jinin iyaye mata yana da nasaba da matsalar kiba da suke fuskanta, amma ga alama hakan ba shi da nasaba da nauyin jikin jarirai sabbin haihuwa.
Sabanin haka kuma, ko da yake a yawancin lokuta, ciwon hawan jini yana da nasaba da matsalar kiba ko nauyin da ya wuce misali, amma nazarin da aka yi a wannan karo ya nuna cewa, idan masu juna biyu suna fama da matsalar hawan jini, to nauyin jikin jariransu bai kai yadda ya kamata ba, lamarin da ya nuna cewa, akwai dalilai masu sarkakiyya da suka kawo illa kan yadda 'yan tayi suka girma a cikin kwan mace.
Masu nazarin sun shirya fadada nazarinsu kan ko illar da nauyin jikin iyaye mata, yawan sukari da ke cikin jininsu da yanayin hawan jininsu suka shafi nauyin jarirai sabbin haihuwa za ta dade cikin dogon lokaci, har ma a duk tsawon rayukan jariran. (Tasallah Yuan)