in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin abinci kamar yadda masu juna biyu suke yi kafin samun ciki yana iya biyan bukatar 'yan tayi
2016-05-08 09:14:39 cri

Masu nazari daga kasar Australiya, sun kaddamar da rahotonsu kan mujallar ilmin sashen kula da mata da mata masu juna biyu na kasashen Australiya da New Zealand, inda a cewarsu, ko da masu juna biyu ba su kara yawan abincin da suke ci ba, jikin su kan shigar da karin Calories. Don haka masu juna biyu ba su bukatar kara yawan cin abinci. Binciken ya nuna cewa cin abinci kamar yadda masu juna biyun ke yi a baya, yana iya biyan bukatun su da na 'yan tayin su.

Masu nazari daga jami'ar New South Wales ta Australia, sun yi amfani da fasahar zamani wajen binciken halin da masu juna biyu 26, a asibitin St George's na birnin Sydney suke kasancewa. Wadannan masu juna biyu sun rika cin abinci kamar yadda suka saba kafin su samu ciki. Amma a lokacin da suka samun ciki, matsakaicin yawan karfin da jikunansu ke bukata a ko wace rana ya karu da kusan kashi 8 cikin dari, kana matsakacin karuwar nauyinsu ya kai giram 10.8, ciki had da yawan kibar da ta karu a jikunasu, wadda ta kai giram 7 baki daya. Lokacin mafi saurin karuwar nauyin jikunan masu juna biyun shi ne watanni shida na farkon lokacin samun ciki.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, dandazon kwayoyin bacteria da ke hanjin masu juna biyu ya sauya sosai, lamarin da ya sanya jikunan su kyautata kwarewarsu, ta shigar da abubuwa masu gina jiki da ke cikin abincin da suke ci, ta yadda ko da ba su kara yawan abincin da suke ci da yawa ba, suna iya kara kiba da yawa.

A ganin masu nazarin, mai yiwuwa ne sakamakon nazarinsu zai musanta ra'ayin da aka dade a kan sa, wato na cewa ya zama wajibi masu juna biyu su kara ci abinci. Haka kuma wata kila nan gaba za a yi kwaskwarima kan girke-girken da ake gabatar wa masu juna biyun domin biyan bukatun su.

Bisa sakamakon nazarin da aka samu ya zuwa yanzu, cin abinci kamar yadda masu juna biyu suka saba, kafin su samu ciki na iya biyan bukatun ginin jikunansu da na 'yan tayinsu. Idan masu juna biyun sun kara ci abinci ido rufe, to, sabanin hakan, za su kara fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sukari, da ma wasu cututtuka yayin samun ciki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China