lafiya1614.m4a
|
Cin abinci tare da 'ya'yansu a karshen mako ya zama ruwan dare ga wasu iyaye a zamansu na yau da kullum. Da zummar kyautata karfin takararsu, wasu dakunan cin abinci suna gabatar da jerin abincin musamman da ake shirya wa kananan yara, inda a cewarsu, abincin na dacewa da biyan bukatun kananan yara wajen gina jikunansu. To ko, yaya gaskiyar wannan lamari?
Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya shaida mana cewa, akwai sauran rina a kaba wajen kyautata ingancin jerin abincin da ake shirya wa kananan yara a dakunan cin abinci a Amurka.
Ko da yake yawan Calories da ke cikin yawancin jerin abincin kananan yara na dacewa, da ma'aunin irin wadannan abinci, sai dai a daya bangaren, yawan kitse da gishiri da ke cikin abincin su kan wuce ma'aunin da ya kamata, wato ba su dace da ma'aunin da aka tsara kan shigar da abubuwa masu gina jikin dan Adam a Amurka ba.
Da zummar yin bincike kan tasirin sinadaran dake cikin irin wadannan abinci dangane da gina jiki, wadanda ake shiryawa kananan yara a dakunan cin abinci, masu nazari daga jami'ar Tufts ta Amurka sun zabi dakunan cin abincin guda 10 masu samar da taune-taune da lashe-lashe, da wasu guda 10 masu samar da abinci iri daban daban a cikin dakunan cin abinci guda dari 1 da ke kan gaba a kasar ta Amurka a shekarar 2014, wadanda mujallar "labaru dangane da abinci da abin sha a Amurka" ta zaba.
Wadannan dakunan cin abinci guda 20 suna shirya wa kananan yara takardar musamman mai dauke da bayanan sunaye da farashi na abinci, inda kuma aka bayyana tasirin sinadaran dake cikin abincin, dangane da gina jiki da yawan Calories da ke cikin sa, da dai sauransu.
Masu nazarin sun gudanar da nazarinsu a tsanake, a karshe sun gano cewa, ko da yake yawan Calories da ke cikin yawancin jerin abincin kananan yaran a wadannan dakunan cin abinci guda 20, sun dace da ma'aunin abincin yaran. Amma yawan kitse da gishiri da ke cikin abincin su kan wuce ma'aunin da ya kamata, wato dai ba su dace da ma'aunin da aka tsara kan shigar da abubuwa masu gina jikin dan Adam a Amurka ba.
Masu nazarin na ganin cewa, kamata ya yi a kara kyautata ingancin jerin abincin da ake shirya wa kananan yara a dakunan cin abinci.
Babu shakka dakunan cin abinci suna rubanya kokarinsu wajen kyautata abincin da suke shiryawa kananan yara, amma akwai jan aiki a gabansu. Za su iya sanya jerin abinci masu gina jiki su shirya wa kananan yaran domin kara samun karbuwa, ta yadda iyaye za su koyar da yaransu, da kuma ba su jagora wajen zabar abincin da ke iya gina jikinsu. (Tasallah Yuan)