in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasancewar kwayoyin cuta masu nau'o'i guda 4 a hanjin jarirai na iya kiyaye su daga kamuwa da asma
2016-04-17 12:22:05 cri

Cutar asma, wani nau'in ciwo ne dake addabar kananan yara sannu a hankali, kuma suna yawan kamuwa da shi. Wasu manazarta daga kasar Canada sun fitar da wani rahoton a kwanan baya cewa, idan jarirai suna iya shakar wasu kwayoyin cutuka nau'o'i 4 masu amfani wadan da ke basu kariya a cikin hanjinsu daga muhallin da suke rayuwa cikinsa, a watanni ukun farko bayan haihuwarsu, to, da wuya su kamu da ciwon asma, wanda idan ya yi kamari, ya kan kawo barazanar mutuwa.

Tun daga shekarun 1950 har zuwa yanzu, yawan masu fama da cutar asma yana karuwa cikin sauri. Mutane na mai da hankali kan ko kamuwa da ciwon asma tana da nasaba da muhallin da ake zama ko a'a? Ko tana da nasaba da shan garin madara a maimakon nonon uwa a matsayin kari ga jariran ko a'a? Ko tana da nasaba da yawan amfani da maganin kau da kwayoyin cuta , ko a'a?

Masu nazari daga jami'ar British Columbia ta kasar Canada sun yi nazari kan mabambantan kwayoyin cutar da ke cikin kashin kananan yara 319. Sun gano cewa, idan jarirai da aka haife sun cika watanni 3 da haihuwa ba su da yawan kwayoyin cutar masu nau'o'i 4 a hanjinsu, to bayan da shekarunsu suka kai 3 a duniya, su kan yi saurin kamuwa da ciwon asma. Wadannan kwayoyin cuta masu kyau masu nau'o'i 4 su ne Lachnospira, Veillonella, Coprococcus da Rothia.

Gwaje-gwajen da masu nazarin suka gudanar kan dabbobi daa wasu berayen sun tabbatar da cewar, gwaje-gwajen da aka yi na shigar da wadannan kwayoyin cutuka iri-iri guda 4 da aka ambata a baya cikin hanjinsu bayan haihuwarsu ba da dadewa ba, da wuya ne su kamu da ciwon asma mai tsanani.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, nazarin da suka gudanar ya tabbatar da cewa, muhalli mai tsabta fiye da kima na iya saurin sanya ciwon asma ya barke. Watanni ukun farko bayan haihuwar jarirai na da muhimmanci kwarai da gaske wajen yin rigakafin kamuwa da ciwon asma. Nan gaba ya dace masu ilmin likitanci su yi la'akari da yin amfani da kwayoyin cutar da ke hanjin dan Adam wajen yin bincike da yin rigakafin ciwon asma. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China