lafiya1604.m4a
|
A kwanan baya ne kungiyar hadin kai ta Cochran mai ofishi a Oxford na kasar Ingila, ta kaddamar da wani rahoto, wanda ke cewa akwai alamu dake nuna cewa an yi karin gishiri game da tasirin amfani da shahararren maganin nan na Tamiflu wajen yaki da mura, don haka ta shawarci gwamnatocin kasa da kasa da su sake yin la'akari da matakin tanadar dimbin maganin.
Maganin Tamiflu, magani ne da kamfanin harhada magani na Roche ya samar domin yaki da mura, a sakamakon barkewar cutar murar tsuntsaye a shekarar 2006, da kuma barkewar cutar mura mai nau'in A na H1N1 a shekarar 2009, lamarin da ya sa gwamnatocin kasashe da dama suka mayar da maganin Tamiflu tamkar magani mai matukar amfani, su ka kuma tanaje shi da yawan gaske.
Duk da haka kungiyar Cochran wadda aka kafa a shekarar 1993 da zummar bai wa sassan ilimin likitanci da mahukunta bayanai game da shawarwari masu zaman kansu, ta tantance sakamakon binciken lafiyar mutane dubu 24, inda ta gano cewa, maganin Tamiflu bai fi sauran makamantan sa amfani ba. Masu binciken kungiyar sun ce maganin na iya sassauta alamun kamuwa da mura, kamar atishawa da tari, da toshewar hanci da dai sauransu. Amma babu isasshiyar shaida da ke tabbatar da cewa maganin na iya hana yaduwar kwayoyin cutar mura, ko kuma ya iya yin rigakafin kamuwa da cututtukan da su kan biyo bayan kamuwa da mura.
Har wa yau kuma, rahoton ya yi nuni da cewa, yayin da ake amfani da maganin Tamiflu wajen yaki da mura, akwai yiwuwar a samu tashin zuciya da amai. Kana kuma, yayin da ake shan maganin a matsayin rigakafin kamuwa da mura, akwai barazanar samun ciwon kai, da haifar da illa ga koda, da tabuwar hankali.
Rahoton ya ci gaba da cewa, bayan shekarar 2009 har zuwa yanzu, yawan maganin Tamiflu da ake sayarwa a kasuwa ya karu cikin sauri. Amma kamfanin Roche bai kaddamar da isasshen bayanan nazari kan maganin ba tukuna. Bisa sabbin shaidu da aka samu daga gwaje-gwaje, kungiyar Cochran da mujallar ilmin likitanci ta Ingila, sun ba da shawara cikin hadin gwiwa, inda a cewarsu, kamata ya yi gwamnatocin kasa da kasa su sake dudduba manufarsu ta sayen maganin na Tamiflu.
Dangane da hakan, kamfanin Roche ya mayar da martani da cewa, ko kusa bai amince da wannan rahoto ba. yana ganin cewa, adadin gwaje-gwaje da aka tanada cikin rahoton bai shafi dukkanin fannoni ba. Watakila shawarar da kungiyar ta gabatar a cewar kungiyar za ta ruda mahukuntan kasa da kasa, tare da sabawa ra'ayi daya da aka rigaya aka cimmawa a fannin kiwon lafiyar al'umma. (Tasallah Yuan)